Labarai

Bidiyo : videon mata da yara da aka sace a niger/sojojin Nigeriya Sun kashe boko Haram 81

Advertisment

‘Yan ta’addan da suka sace mutane 21 a jihar Neja sun fitar da wani bidiyo da ke dauke da wadanda suka kama suna neman da a bawa yan ta’addan fansar Naira Miliyon Dari Biyar, kamar yadda fitaccen marubuci Ahmed Salkida ya wallafa bidiyon a shafinsa na Twitter
 
Ga wani karin bayyani
 
SUBHANALLAH
‘Yan ta’adda sun sace mutane a garin Yakila karamar hukumar Rafi jihar Niger, sun dauke su a bidiyo suna kira ga Gwamnatin Nigeria ta biya su kudin fansa Naira Miliyan 500
Wanna aikin ‘yan Boko Haram ne ba shakka kuma mutanen Shekau, sune da wannan salon, sunyi tasiri sosai a cikin masu garkuwa da mutane, talauci ya kama Shekau yana neman kudi ta kowani hali
Muna rokon Allah Ya aminar da wadannan mutane daga cutarwan ‘yan ta’adda, Allah Ka kawo mana karshen wannan masifa Amin
Ga bidiyon nan kasa
https://youtu.be/Y5SYPyaXV-U

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button