Labarai

An gano Dazuka 5 da ‘yan ta’adda ke amfani da su wajan aikata laifuka a Najeriya

Dazuka na taka muhimmiyar rawa wajen inganta rayuwar dan adam da dabobi. Itatuwan da ke cikinsu na zame wa ‘yan adam abinci da magani da makashin wuta da sauransu.
Haka ma, dazuka na taimaka wa wajen adana igancin kasar noma, sassafa iskar da mutane ke shaƙa, kare gusowar Hamada da rage dumamar yanayi. Dazuka gidajen ne ga manun daji, kuma wuraren shakatawa da bude ido ga ‘yan adam.
Ubangiji Ya albarkaci Najeriya damanya-manyan dazuka. Kimanin hekta miliyan 10 na fadin kasar, wato kimanin kashi 10 na fadin kasar baki-daya, daji ne.
Dokokin Najeriya ware kimanin dazuka 445 a fadin kasar a matsayin wuraren da aka haramta farauta da saran itace da sauran sana’o’i da ka iya kawo barazana ga dazukan.
Sai dai duk da alfanunsu, da dama daga dazukun Najeriya sun zama maboyar ‘yan bindiga da dabarayi da ‘yar ta’adda da masu garkuwa da mutane. Manya-manya daga wadannan dazuka da ke arewacin Najeriya sune:
Dajin Sambisa
A yanzu wannan daji shi ne ya fi kowanne suna a Najeriya domin kuma a cikinsa ‘yan ta’adda Boko Haram suka samu mafaka. Wannan daji ya samo sunansa ne daga sunan kauyen “Sambisa” da ke cikin Karamar Hukumar Gwaza ta jihar Barno.
Dajin yana nan kimanin kilomita 60 daga kudu-mosa-gabashin garin Maiduguri, kuma yana da fadin kimanin murabba’in kilomita sama da 2,200 da ya mamaye wasu bangarorin jihojin Barno, Yobe, Gombe, Darazon jihar Bauchi, Jigawa har dangana da dajin Fargore da ke jihar Kano. Amma fadin dajin ya yi ta raguwa saboda tasarrufin bil adama har ya dawo kimanin murabba’in kilomita 600 a yanzu.
Allah Ya albarkaci Dajin Sambisa da yanayi mai dadi da manyan bishiyu da dagin tsuntsaye har kala 62. Haka kuma dajin yana da manyan namun dawa irinsu goggon biri da giwaye da zakuna da damusa da kura da dai sauransu.
‘Yan Boko Haram sun kutsa dajin Sambisa ne tun shekarar 2009 bayan dauki-ba-dadi tsakaninsu da jami’an tsaro a garin Maiduguri wanda har ta kai ga kasha ‘yan kungiyar a kalla 200.
Daga nan Abubakar Shekau da mabiyansa suka maida wannan daji sansaninsu. Anan suke buya suna kitsa hare-haren; anan suke garkuwa da mutanen da suka sata; anan kuma suke noma abincinsu da dai sauran harkokinsu.
Dajin Alargona
Dajin Alagarno daji ne da yayi kaurin suna cikin shekarar nan domin hare-haren da dakarun Najeriya ke kaiwa makayan Boko Haram da suka wannan dajin maboya. Bayan yagewar Boko Haram zuwa gida biyu a 2016, gwamandojin da suka yiwa shekau suka ji tsoron cewa Shekau zai sa a kashe su, kuma gashi a lokacin ba su da kafi sosai. Saboda haka suka bar dajin Sambisa suka koma Dajin Alagarno. Duk da yake yanzu ISWAP tayi karfin sosai har ta girka sansanoni a Sambisa da Tafkin Cadi, wandansu mayakan ISWAP sun ci gaba da zama a Dajin Alagarno, mai yiwa saboda fadin Bahaushe “Gida biyu maganin gobara”.
Alagarno daji ne da ke zaune cikin Karamar Hukumar Mobbar, kimanin kilomita 150 arewacin garin Maiduguri, kuma ya nausa har cikin wani bangaren Karamar kuhumar Geidam ta jihar Yobe. Haka kuma dajin yayi iyaka da Jamhuriyar Nijar. Ta wannan daji ne mayakan Boko Haram suka kai hari garin Damasak har suka yanka mutun 70 a Mayun 2015.

Dajin Rugu
Rugu sunan wani jarumin shugaban al’umma ne da aka taba yi a kasar Katsina. Gogan yayi suna wajen farauta da jarumtarsa wajen yaki har akan yi masa kirari da cewa “Rugu Kan Kura Kowa ya taba ka zai kwana lahira”.
Shi wannan bawan Allah da mutanensa sun zauna ne a wani daji wanda a yanzu yake cikin Karamar Hukumar Safana ta Jihar Katsina. Saboda haka sai aka sanya wannan daji sunansa wato Dajin Rugu.
Dajin Rugu na da duhuwar dogayen ciyayi da manya bishiyu musamman lokacin damuna. Dajin na da girman gaske kuma ya malalaya tun daga kasar Katsina har Birnin Gwari a kasar Kaduna ya kuma keta wani bangaren jihar Zamfara.
Kamar Sambisa, Dajin Rugu ya yi suna da zama gidan zakuna da giwaye da kuraye da birrai da jakunan dawa da sauransu.
Sai dai a Shekarun baya-bayan nan, Dajin Rugu ya canza daga gurin yawon shakatawa da bude ido zuwa abin tsoro da firgici.
Ya zama sansanin mugayen barayi da ‘yar bashi da masu garkuwa da bayin Allah. Ko da yaran 344 da aka sace daga makarantarsu a garin Kankara a wata Disembar da ta gabata, Dajin Rugu aka kai su aka boye.

Dajin Kamuku
Kamuku sunan wata ƙabila ce da ke kudancin Kaduna. Sakancewar Kamuku daya daga cikin al’ummun da ke makotaka da wannan daji ya sa ake kira dajin Dajin Kamuku.
Dajin Kamuku yana cikin kasar Birni Gwari ne kuma Kogin Mariga ya raba su da Dajin Kuyambana da ke kasar Zamfara da Kebbi.
Shi ma wannan daji yana da manyan itatuwa masu duhuwa da manya namun dawa da kuma dangin tsunstaye ‘yan gida da kuma baki har kimanin 177.
Dajin Kamuku ya zama dodo ga al-ummar gurin da ma baki. Har ma mazauna wurin kan yiwa Kamuku lakabi da “Sambisa” saboda firgicinsa.
Wannan daji da kuma Dajin Kuyamban sune mazaunin ‘yar bindigan da suka addabi kasar Birnin Gwari da matafiya Abuja.
Marasa imanin sai su shigo cikin gari ko su tare hanya suyi aika-aikarsu sannan su shige cikin Kamuku su boye abinsu.
Dazukan Nasarawa da Neja
Akwai dazuka da dama a jihohi Nasarawa da Neja har ma da Kogi da suka fara kaurin suna kwanan nan saboda karuwar hare-haren ‘yan bindiga da ma masu da’awar jihadi.
Wadannan dazuka sun hada da Dajin Unaisha da kuma Dajin Uttu a Karamar Hukumar a jihar Nasarawa da Dajin Gegu dake a jihar Kogi.
Akwai kuma Dajin Tagina da ke jihar Neja in nan ne ake zaton ‘yan bindigan da suka sace dalibai da malaman makarantar Kagara ke garkuwa da su.
MeYasa Masu Laifi ke Amfani da Wadanna Dazuka?
Akwai dalilai da dama da suka bai wa masu laifi damar amfani da wadannan dazuka. Cikin har rashin kula daga gwamnati.
Babu jami’an tsaro ko na gwamnati a mafi yawa wadannan dazuka. Kuma gashi ba hanyar mota balle jami’an tsaro su samu daman shiga.
Su ma kansu masu laifin da Babura suke amfani. Sannan kuma ga duhuwa da koguna da duwatsu da kwazazzaɓai a cikin da yawa da wadannan dazuka.
BBChausa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button