Kannywood

Binkice: Falalu A Ɗorayi yana Daga Cikin Yaran da Darakta Ashiru Na Goma ya koyar da su yadda ake Daraktin A Film

Bayanan bayyanar rahoton rashin lafiyar daraktan shirya fina finai na Kannywood ashiru nagoma jaridar demokradiya sun wallafa wani rahoto Kamar haka.
“Wakilinmu Mu’azzam Yakubu Sanka
Darakta Ashiru na goma ba ɓoyayyen mutum ba ne da sai an yi maka wani sharhi game da shi ba abin sani kawai shine Yana daga cikin haziƙan Daraktocin Hausa Film ko mu ce Kannywood a yanzu wanda a Baya ya bayar da tasa gudummawa wajen Habbaka harshen Hausa mutuƙa.
Cikin abinda wannan bawan Allah yayi shine har da horar da wasu daga cikin yaran sa a wancan lokacin yadda ake gudanar da wannan Sana’a ta Film kuma daga cikin haziƙan da ya koyar akwai mashahurin Daraktan nan Falalu A Ɗorayi, da Musa mai Sana’a, wanda suna daga cikin manyan Yaran sa.
Amma yanzu haka Ashiru na Goma ya samu Cutar Taɓuwar Hankali wato Hauka kamar yadda kuke Gani A Hoto na uku kuma babu wanda ke kula da shi ko taimaka masa a Rahotannin da muka samu yanzu.
Tambayoyin da kowa ke yi a nan su ne, wai ina waɗannan Abokan sana’ar ta shi, kuma Ina yaran da suka zauna ƙarƙashin shi ko kuma mu ce Waɗanda ya koyar da su?
Jaridar Dimokuraɗiyya ta Baza komarta domin zaƙulo muku waɗannan Mutane da muka ambata don jin ta bakin su.
Ku Saurare mu!
Ga mai buƙatar ya sanar da mu wani lamari game da wannan zai iya kiran 08099124425, Ko kuma yayi WhatsApp”.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button