Ɗadi Kashe Ni! Hamshakiyar attajira, Sahoo Bint Abdullah Al-Mahboub, ta auri direbanta (Bidiyo)


Wani bidiyo da ya yadu a kasar Pakistan wanda ke nuna daurin aure tsakanin wani mutumi da sabuwar amaryarsa ya janyo cece-kuce a kafafen ra’ayi da sada zumunta.
Netizens da kafafen yada labarai a Pakistan sun bayyana cewa matar da aka gani cikin bidiyon wata hamshakiyar attajira ce yar kasar Saudiyya, Sahoo bint Abdullah Al-Mahboud, yayinda kuma mijin da ta aura direbanta ne.
Legit na ruwaito bincike ya nuna cewa lallai matar itace Sahoo wacce ke da mallakin dukiyoyi a fadin duniya musamman Makkah, Madina, da kasar Faransa.
Hakazalika an yi kiyasin cewa arzikinta ya kai dala biyan takwas ($8bn).
Sahoo Bint Abdullah Al-Mahboub, Businesswoman whose wealth is estimated at 8 billion$. She owns residential properties and hotels a lot in Mecca and Medina, as well as towers in France and others. She marries her Pakistani driver. pic.twitter.com/tQ9PFzHXN3
— Imran (@hassanjutt25) January 1, 2021


