Uncategorized
Wuff : An Tsayar Da Ranar Daurin Auren Matashi Dan Kano Da Kuma Masoyiyar Sa Baturiya (Hoto)
Advertisment
Hausawa kance karshen alewa kasa shikenan suleman zai zamo mijin baturiya wanda shafin arewablog shima dai ya wallafa wannan labarin wanda yayi matukar daukar hankali mutane.
Tun a watannin baya Akaso daura wannan aure amma annobar Corona Virus ta dagatar da wannan abin Alheri inda tasa dole a dage daura wannan aure har zuwa lokacin da wannan annobar zata lafa.
Masoyan guda biyu sun hadune akafar sada Zumunta ta Instagram yayinda wannan baturiya taga hotunan wannan matashi kuma taga yana kaunarsa hakan yasa ta taso tundaga garinsu har zuwa birnin Kano domin yiwa sahibin nata kallon qurilla kuma ta gamsu yadda tasamu tarairaya da kuma kula irin ta masoyi duk da cewa ita wannan matar ta girmi wannan matashi.