Uncategorized

Chadwick Boseman: Cutar daji ta kashe tauraron fim na Black Panther

Tauraron fina-finan Amurka Chadwick Boseman, wanda ya taka muhimmiyar rawa a fim din Black Panther, ya mutu sakamakon cutar daji, a cewar iyalinsa.
Tauraron mai shekara 43 ya mutu ne a gidansa da ke birnin Los Angeles kuma matarsa da ‘yan uwansa suna kusa da shi lokacin da ya cika.
Boseman bai bayyana wa duniya cutar da ya yi fama da ita ba.
“Chadwick gwarzo ne wanda ya jure sosai, sannan ya fito a fina-finai da kuke matukar kauna,” a cewar iyalinsa a wata sanarwa da suka fitar.
“Daga fim din Marshall zuwa Da 5 Bloods, da fim din August Wilson Ma Rainey na Black Bottom da kuma fina-finai da dama – dukkansu an dauke su yayin da yake fama da tiyata daban-daban da kuma gashin da ake yi wa masu fama da cutar daji. Abin alfahari ne a gare shi da ya taka rawa a matsayin Sarki T’Challa a fim din Black Panther.”
Kauce wa Twitter, 1

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1
Sunan Boseman ya fito ne a rawar da ya taka ta kwaikwayon fitattun mutane irin su Jackie Robinson a fim din 42 da aka yi a 2013 da mawaki James Brown a fim din Get on Up da aka yi a 2014.
Sai dai ya fi shahara a fim din Black Panther da aka yi a 2018.bbchausa.com na ruwaito
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button