Ummi zeezee Tayi Korafi kan kin Taya Rahama Sadau Murnar “Birthday” Da Yan Kannywood basu yi ba
A yau ne 7/12/2020 take ranar haihuwar ta murna shekara ashirin da bakwai da haihuwa (27yrs) wanda tun farko wannan wata tayi sanarwa cewa wannan wata ne ranar haihuwarta.
Wanda ba’a ga anyi tururuwa wajen tayata murna zagayowar ranar haihuwarta ba kamar yadda anka saba ba.
Koda yake yan uwanta makusantan ta tsiraru da abobanta kadai ne suka taya ta murna ba kamar yadda anka saba ba.
Wanda har shine yasa tsohuwar jaruma ummi zeezee na Wallafa hoton rahama sadau da rubutu kamar haka:-
“I keep on wondering since morning ,yau birthday din actress “RAHAMA SAUDA” ammah kaf yan masana-antar kannywood banga sunyi posting pictures dinta domin tayata murnar birthday din nata ba.so what is the REASON please?koma dai menene dalili she is still a MUSLIM tana sallah tana yiwa annabi Muhammad s.a.w.salati dan haka koma me nene you guys should forget about it and let her MOVE ON !! Happy birthday princess#may allah forgive us all !!!ameen @rahamasadau”






