Labarai

Yanzu – Yanzu: Kotu Ta Bada Belin Sanata Ali Ndume

Advertisment

 
Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta ba Sanata mai wakiltan Borno ta kudu, Ali Ndume, wanda aka tsare a kurkuku tun ranar Litinin beli a yau Juma’a.
Alkalin Kotun mai Shari’a Okon Abang a hukuncin da ya yanke yau Juma’a ya ce ya yanke shawarar ba Sanata Ndume beli ne saboda tarihinsa na mutum mai halayya nagari amma ba dan uzurorin da ya gabatar ba.
Alkali ya bashi beli ne kafi kotun daukaka kara ta saurari karar da Ndume ya shigar ranar Litinin domin kalubalantar hukuncin jefa shi kotu kan gaza kawo Maina kotu.
Ya umurci Sanatan ya kawo wanda zai tsaya masa kuma ya kasance mazauni Abuja kuma mai dukiya a Abuja. A cewar Alkali, wanda zai tsayawa Sanatan wajibi ne ya rantse cewa zai sadaukar da dukiyarsa idan Sanatan ya gudu.
Majiyarmu ta samu daga shafin Manuniya,bayan haka, Alkalin ya umurci Sanatan ya sallama fasfot dinsa ga magatakardan kotun. Bugu da kari, ya umurci Sanata Ndume ya yi alkawarin zai mika takardun daukaka kararsa zuwa kotun daukaka kara cikin kwanaki 10.
Alkali ya garkame Ali Ndume a kotu ne bayan wanda ya tsayawa a kotu, AbdulRashid Maina, ya gudu. Maina, tsohon shugaban kwamitin gyaran lamuran fansho, yana gurfana a kotu kan zargin almundahanar makudan biliyoyi.
A ranar 18 ga Nuwamba, 2020, Alkali Abang ya janye belin da ya ba Maina kuma ya bada umurnin daureshi.Bayan an nemi Maina an rasa, Alkali ya ce a garkame Ndume a kotu maimakonsa ko ya biya kudi Miliyan 500.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button