Bincike: Dagaske Ne Idan Namiji Yayi Jima’i Da Mace Ya Gama Da Ita?
Wannan tambayar ta jima tana yawo a tsakanin maza da mata ba tare da samun cikenken amsa ba daga bangarorin biyu na maza da matan.
Sai dai idan aka kasa mata kashi 100 kashi 99 sun yarda da cewa muddin namiji ya kwanta da su, ma’ana ya sadu da ita saduwa irin na jima’i har abada ya gama da wannan matar.
Wannan tunanin yayi matukar tasiri bama ga maza da mata mazinata ba, a’a tasirin ya karada har cikin matan aure masu jima’i da mazajensu ta hanyar aure duk sun yarda da cewa tunda dai mazansu sun kwanta dasu to ai babu sauran wani abunda za a boye musu.
Wannan tunanin yayiwa mata musamman ‘yan mata illa sosai, illar da yana da matukar gaske a iya gyarawa muddin ba ta irin wannan binciken ba.


Domin ‘yan mata suna fadawa harkar zina ne gadangadan da samarinsu bayan sun musu yaudara na farko sun samu kansu. Daga nan sai ‘yan matan suke dauka tunda dai har ya santa a ‘ya mace to yangan mai zata masa ko rowan mai kuma zata masa. Da wannan tunanin ne sai tayi ta bada kanta yana zina da ita son ransa a lokacin da kuma ta saba da zinar idan ya zamanto wannan saurayin baya kusa duk wanda shedan ya baiwa sa’a yana latsata zata mika yuwa daga nan kuma shikenan ta shahara ta bunkasa zina kawai.
Zaka yi mamaki mata har masu manyan shekaru ma sunada wannan tunanin. Wanda yasa wasu mata suke yiwa ‘ya’yansu mata hudubar kada su rika baiwa mazansu hadin kai ako yaushe a cewarsu hakan yakan kawo raini.
Har ila yau wannan camfen ko tunannin yayi tasirin da samari masoya da suka soma soyayyarsu da kyankyawan niya na aure da shedan ya shiga tsakanin sunyi zina da juna shikenan sai wannan ya zama sanadiyar rugujewar maganar auren nasu saboda yadda duk wani sauyi data gani daga wajen saurayin sai ta dauka cewa saboda ya riga ya santa ‘ya mace ne yasa ya canza shi kuma yana iya fakewa da wannan ya samu hanyar guduwa.
Wannan tunanin yayi tasiri matuka da za a ji mata suna kokawa cewa saboda sun yi zina da saurayi ya gujesu. Haka kuma za a ji matan dai suna kukawa cewa saboda sunki yin zina da saurayi ya gujesu. Daga nan mai karatu zai fahimci jima’i da ‘ya mace bashi yake sawa namiji ya tsaya ko ya gudu ba.
Mata daga yau da kika karanta wannan sharhin nazarin binciken ki cire wannan tunanin a ranki na muddin namiji yayi jima’i dake ya gama dake, sam ba haka abun yake ba. Ga kuma yadda abun yake kamar haka.
A darusan mu na baya munyi bayanin abubuwan da suke iya tadawa maza sha’awarsu na jima’i. Yayin da sha’awar na miji ya motsa gaba daya hankalinsa yana natsuwa ne wajen kokarin kyautatawa macen da yake tare da ita. Don a haka a wannan lokacin haba-haba zai rika yi mata. Wasu mazan duk wani umurnin da mace ko bukatar ta a wannan yanayin yana iya biya matasu muddin zata kwantar masa da wannan sha’awar tashi ta hanyar jima’i.
Shi namiji ba kamar mace yake ba, kashi 60 cikin 100 na maza da zarar sun samu biyan bukata da mace abu na gaba da suke bukata shine su samu damar da zasu sharara barci a irin wannan yanayin ne mazan suke saurin zame jikinsu daga cikin mace ba tare da damuwa da nata gamsuwarba daga bisani sai kuma ya janye jikinsa daga gareta domin neman kadaita ko yayi barci.
A irin wannan yanayin mata suna bukata ne a rungumsu koda za ayi barci ne, wasu ma bukatarsu shine a bar azzakarin a cikin farjinsu na wani lokaci kamin a zare. Saboda ita mace kamar yadda mukayi bayani a baya, kamin namiji yayi zuwan kai sau daya wata macen tayi uku tana kuma shirin kara wani uku koma fiye, kashi 15 ne daga cikin mata suke samu kasala da zaran sun biya bukata cikin kashi 100 na binciken da aka gano.
Ma’ana da zaran haka ya kasance da mace a farko kamin kayi kanata lanlabanta, kana mata bauta sai gashi tana baka kana samun biyan bukata bamakaso tayi kusa da kai, kama rabuda ita can gefe kana barci. Ko kayanta da kayiwa dai-dai yanzu itace ke bi tana tsincewa tana maidasu jikinta ba tare da taimakonka ba. Daga wannan lokacin mace ki tunanin cewa ai saboda saninta da kayi a yanzu shi yasa kayi mata haka. Sai dai ba haka bane. Da zata barshi zuwa wani dan lokaci sha’awarsa ya sake motsawa, wannan bauta da hidmar da yayi a baya shi zai sake yi, kuma da zaran ya samu gamsuwa hakan kuma zai sake yi.
Abunda yawancin mata basu fahimta ba shine, a duk lokacinda namiji yake sha’awarki a lokacin ji yake tamkar bai taba saninki ‘ya mace ba. A wannan lokacin ke da macen da bai taba ganin tsiraicinta duk daya kuke a wajensa ko da kuwa kunyi shekaru nawa kuna jima’i.
Sai dai da yake an riga anyiwa mata illa a tunaninsu na duk namijin da ya sansu a mace ya gama dasu, da wannan ne basa iya kin amincewa da mazan idan suna bukatarsu musamman ta zina. Da wannan ne mazan suke musu ga dodo ga dodo nan na cewa ‘yangar mai zaki mini bayan na gama dake’. Karya ne gobe idan ya dawo ki hanashi kiga yadda zai yita magiya tamkar yanzu kuka soma haduwa. Akwai matan da idan suka hana mazajensu jima’i dimaucewa suke. Akwai mazanda idan suka saki mace binta suke sau da kaya bama jima’i suke bukata ba, inama zata masa kiss ko ta rungumeshi shi bukatarshi ta biya. A baya da matarsace, babu yadda bai sarrafata ba idan ya gama da ita mai yasa yanzu yake marmarinta?
Akwai samari da budurwarsa zata ki amincewa da yin zinar dashi bayan yayi sau daya tace sai sunyi aure ko kuma ya daina kulata ta daure da cire tunanin ya gama da ita, dole yayi guda, ko ya zo a daura auren don ya dandana ko kuma ya kama gabansa ita ta dauki darasi daga nan.
Baya ga wannan dabi’a da alada na maza a jima’ince da suke amfani dasu wajen yiwa mata wayo, akwai wasu dalilai na asali da kan iya jawo namiji ya gujeki bayan ya sanki ‘ya mace.
A darasin mu na gaba zamu kawosu tare da cikenken bayaninsu. Amma kamin nan. Mata daga yanzu ku cire tunanin duk namiji daya sanki a mace ya gama dake, an jima ana muku illa da wannan. Idan da zina ya sanki ki dauka kinyi kuskure ne daga yanzu ki ce bazaki bashi ba kuyi aure.
Namiji baya iya gamawa da mace saboda ya santa a ‘ya mace. Kawai an cusa muku tunanin ne kamar yadda aka cusawa maza tunanin cewa wata mace tafi wata dadi.