Labarai

Tsarin “INKSNATION” Jama’ar Arewa Ku Fadaka ~ Daga Datti Assalafiy

Wannan shine karo na biyu da zanyi dogon jawabi akan wannan tsari na INKSNATION wanda kusan kowa yanzu ya san dashi, domin a yanzu babu wata jiha ko karamar hukuma da basu da wakilai da suke ta yiwa jama’a rijista

A rubutu na farko na sha zagi, suka, gatse da karyatawa daga gurin wadanda suka tsunduma a harkan INKSNATION, sai dai ni zagi da tsinuwa da batanci baya sanyaya zuciyata, karfin zuciya yake kara min da kaimi

Har na yanke shawaran ba zan sake cewa komai a kan INKSNATION ba saboda kada masu son abin su zargeni da hassada ko ina musu kyashi, to amma sirrin INKSNATION da na sani, kuma ina ji ina gani za’a cutar da ‘yan uwana, idan na zauna ina kallon yadda suke cigaba da rungumar INKSNATION din bakin ciki da tausayi yake lullube zuciyata, wannan dalilin yasa zan sake yin magana

Lamarin ‘yan Arewa sai Allah, mafi yawan mutanen mu na Arewa basa fahimtar abubuwan cutarwa da sharri da damfara da ake ankarar dasu a kai, sai idan ya samesu sun dandana kudarsu suke fahimta, kamar misali da dikikin yaro da baya gane karatu ne sai yaji duka tukunna, haka wasu suke a Arewa, wallahi kishin ‘yan Arewa ya sa zan sake magana akan INKSNATION ba wani abu ba

Waye Mamallakin INKSNATION???
Wani matashi ne bayarbe ‘dan jihar Lagos talakane kamar kowa yayi karatu babu aikin yi, sai ya kwanta bacci kamar yadda yace, a cikin baccinsa sai yayi mafarki da Allah, wai Allansa ya nadashi matsayin Annabta, kuma ya bashi iko da umarni yayi kira ga talakawan  Nigeria da duniya ya fitar da su daga kangin talauci

Daga hakane aka wayi gari ya fara da’awar Annabta a bayyane, ya hadu shi da abokansa suka kirkiri wannnan tsarin kamfani da ake kira INKSNATION wanda da shi ne zasu raba talakawan duniya da talauci kamar yadda suke fada muku, lamarin nasu ba wai iya Nigeria bane, duk duniya suke ikirari

Datti Assalafy ya kara da cewa ,jama’a matashin nan ba mai bin addinin nasara da gaskiya bane, yafi alaka da kungiyar asiri masu bautar shaidan da zai raba mutane da addini, yana kira cewa a hadu Mabiya addinin nasa da Musulmi da masu addinin tsafi da bautar dodo da wadanda ba suyi imani da kowani irin addini ba wai a hadu a zama daya

Kunga a addininance mutum bai kamata yazo ko da kusa da su ya kulla kowace irin alaka da su ba, to a fakaice wannan shine hanyoyin dabara da ‘yan kungiyar Masoniyyah (Freemasons) suke amfani dashi wajen halakar da mutane

Kuma zuwa yanzu dukkan alamomin haka da yake boyewa sun fara bayyana a kanshi, a zoom meeting ta kafar yanar gizo da yakeyi da wakilanshi a sassan jihohin Nigeria ya fara kiransu da suyi watsi da addini a rungumi Humanity kawai

Ya kai ‘dan uwa ‘dan Arewa Musulmi da duk wani mai hankali ka tsaya kayi tunani, shi wannan da ya kirkiri INKSNATION wanda yace idan kayi rijista da naira 1000 ko 1500 zaka samu dubban daruruwan Naira ko miliyoyin kudi, kowa yayi dogon tunani da nazari akan wadannan abubuwa guda biya da na lissafa a kasa don Allah
?
1-A ina yake da kudin da zai cire mutanen duniya daga talauci alhali kafin ya samar da INKSNATION talakane tukuf?

2-Shi fa ba gwamnati bane, talakane a farkonsa, kuma tun tarihin duniya ba’a taba samun wani attajiri ko wata gwamnati da ta fitar da mutanen kasarta daga talauci ba gaba dayansu, mai INKSNATION ya haka?

3-Shi ba ‘dan kasuwa bane, ba wani attajirin mai kudi bane da za’ace yana da kudin da zai iya rabawa talakawan duniya da talauci, ko a duniyar mahaukata ya kamata mahaukata su yadda da kiran mai INKSNATION?

4- Shin ko gwamnati ta isa ta raba mutane da talauci? A kasar Amurka ma akwai talakawa suna kuka kamar yadda talakawan Nigeria ke kuka, duk da kasancewar Amurka a matsayin kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya, Mai INKSNATION yafi Amurka kudi ne?

5-To amma yau ga wani yaro matashi yana da’awar shi Annabin Allah ne zai fitar da talakawa daga talauci, anya lafiyayyar kwakwalwa mai hankali ya kamata ta yadda da wannan?

To zan fasa muku sirrin kuji yadda abin yake jama’a

Wannan tsarin na INKSNATION babban damfarace da ha’inci suka zauna suka tsara domin su arzurta kansu ta hanyar wayo da dabaru irin na masana ilmin kimiyyar damfara, wanda idan sun tashi tsara wannan gagarumar damfara mai lasisi suna hada baki da wasu gurbatattu daga cikin jami’an hukumar EFCC, suna hada baki da wasu maciya amana da suke aiki da babban bankin Nigeria CBN, suna hada baki da kungiyar NGO, suna hada baki da kamfanonin da suke kwangilar tura kudi ta yanar gizo wato “Payment Gateway” irinsu:
-Paystack
-Flutterwave
-GTPay
-Remita
-Interswitch Webpay
-Voguepay
Da sauransu, cewa idan mun shirya damfara aka samu biyan bukata kuna da kaso kaza

Misali:
Idan an shirya damfarar mutane cewa duk wanda yayi rijista da Naira Dubu daya zai samu Naira dubu dari, mutane sun yadda saboda sunga kamfanin yana da rijista da CAC, kuma kamfanin da zai biya mutane kudi (Payment gateway) misali kamfanin Paystack ai yana da rijista da babban bankin Nigeria CBN, kuma munga EFCC basuyi tsawatarwa a kai ba, don haka mu jama’a mun amince da wannan kamfanin sahihi ne, bari mu biya kudin rijista naira dubu daya domin mu samu ribar Naira dubu dari ko sama da haka

To sai aka wayi gari mutum miliyan daya sun biya dubu daya sunyi rijista, shi kuma kamfanin damfarar idan ya lura ya tara biliyoyin Naira, sai ya fara biyan mutane kalilan kamar da gaske, domin jama’ar da ake so a damfara su saki ciki su rungumi abin da gaske, ana nan sai kamfanin ya dakatar da biya, sai yace an samu ‘yar wata matsala kadan, jama’a suyi hakuri za’a cigaba da biya zuwa wani lokaci, suyi ta jan ra’ayi, can kuma mutane suna ta rijista, idan tafiya tayi nisa sai kamfanin ya fitar da sanarwa cewa ya ruguje, EFCC sun rufe suna bincike

Shikenan sai ayi dodorido, wasu gurbatattun jami’an EFCC da kamfanin damfarar ya hada baki dasu su karbi kason su, wasu gurbatattun ma’aikatan CBN da kamfanin damfarar ya hada baki dasu su karbi kason su, hakanan kamfanin Payment gateway ya karbi nashi kason, sai ayi wani abu kamar ana bincike da gaske, har a biya wasu jaridu su yada labari, zuwa wani lokaci a shashantar da maganar, ku kuma shikenan jama’a an cinye kudaden da kukayi rijista sai a lahira kuma

Jama’a ina mai tabbatar muku da cewa wannan jawabin da nayi shine sak da abinda zai faru da wannan kamfani na damfara wato INKSNATION watan watarana ba da jimawa ba da zaran sun samu adadin abinda suke nema sai haka ta faru

Akwai wani bincike da nakeyi akan kasuwanci ta yanar gizo wanda a turance ake kira da Digital Economy, ko Connected Economy ko kuma Internet Economy, yanzu a duniya babu kasuwancin da ya kai wannan riba, misali da mai mallakin kamfanin Facebook wato Mark Zuckerberg, Facebook Digital Economy ne, yanzu batun da ake Mark Zuckerberg yana dab da kamo Bill Gate mai kamfanin Microsoft kudi a duniya, Mark Zuckerberg ba wani abu yake sayarwa ba, ko allura bai sayarwa, ni da kai da ku yake hadawa a Platform dinsa na Facebook idan mun sayi data muka hau online yake cin riba da mu

Don haka a ka’idar Connected Economy da nake bincike a kai a duniya yace duk wani harkan kasuwanci na yanar gizo da za’ace ka kayi rijista ko ka saka kudi naira 1000 daya zaka samu Naira 1500 ba tare da kayi komai ba, to wannna harkace ta damfara da ha’inci tsantsa ba gaskiya a cikinta, ko an fara zai wargaje a lakume kudin wasu, amma duk wani kasuwanci na yanar gizo sahihi da sai ka aikata wani abu kasha wahala kafin a samu riba a raba to wannan mai kyau ne

Don haka jama’ar Nigeria musamman
‘yan uwa na Arewa me kukayi da INKSNATION zasu biyaku da Miliyoyin Naira idan kukayi rijista da naira 1000 kacal?, ko suna da injin buga kudi ne?
Wannan INKSNATION din ba komai bane face tsantsar ha’inci da damfara, sunyi amfani da halin da kuke ciki na talauci suna karbe muku kudade suna tarawa suna arzurta kansu

Ina bin diddigin duk abinda yake wakana a INKSNATION, yanzu haka akan Data-base din mai INKSNATION din yana da mutane kusan Miliyon hudu da sukayi rijista, ya riga da ya tara biliyoyin Naira, kuma kashi 90 cikin 100 na mutanen da sukayi rijista dashi ‘yan Arewa ne

Muna kira ga Malamai da ake jin muryoyinsu, muna kira ga gwamnonin Arewa da Sanatoci da ‘yan majalisu, hakkine ya rataya a wuyanku da kuyi bincike akan INKSNATION ku dauki matakin gaggawa da ya dace

Allah Ya sauwake

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button