Uncategorized

kuskuren Da Ya kamata Shugabanni da ‘Yan Boko Musulmai Su Gyara~ Datti Assalafy

Jiya Maigirma gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya fitar sa sanarwa a shafinsa na Facebook cewa yana karanta wannan Littafin wanda wani bature ya rubuta a kan tsarin gudanarwan gwamnatin kasar Kaduna daga shekarar 1800 zuwa 1950 Miladiyyah

Gwamnan yace yana duba Littafin ne domin ya taimaka masa wajen zaben sabon Sarkin Zazzau

Jama’a wannan babban kuskure ne da aka jima ana yinsa a Nigeria tsakanin mutanen da suke kiran kansu Musulmai, saboda abinda sukeyi bisa ga takaituwa da dogaro akan abinda turawa suka rubuta na tarihi ko bincike akan Musulunci da jihadi

Mafi girman kuskure da gwamnan jihar Kaduna zaiyi wajen neman madogara akan tarihin Daula da Sarakunan Kasar Zazzau  gabannin shigowar turawan Mulkin Mallaka shine takaituwa zuwa ga abinda yake kunshe a cikin wannan Littafin da bature ya rubuta

Da jimawa na karanta wani yanki na wannan Littafin, akwai gurin da baturen ya bada tarihin yadda mayaka mujahidai na Shehu Usman Dan Fodio kabilar Fulani suka shigo Kasar Zazzau da yaki, suka yaki Sarkin Zazzau wanda yake Musulmi, wai basu farmasa ba sai a daidai lokacin da ya fita sallar karamar idi, daga nan ne suka fara sarautar Fulani

Wannan Littafin da Malam Nasir yake karantawa akwai karya da kura-kurai masu tarin yawa a cikinsa, Shehu Usman bai yaki Musulmai ba, bidi’ar da yazo ya tarar Musulmai nayi ya yaka da hujja na ilmi ba makami ba, amma ya yaki maguzawa da kafurai da suka farmasa, wanda wannan shine jihadin Musulunci

Jihadin Shehu Usman turawa sun lalata tarihinsa, yadda turawa suka rubuta tarihinsa zaku ga bai da maraba da jahadin Abubakar Shekau na Boko Haram, haka yahudawa da nasara suke wajen kokarin lalata tarihin mutanen kirki har da Annabawan Allah

Hatta tarihin Manzon tsira Annabi Muhammad (SAW) sai da suka lalata, sun rubuta tarihinsa cewa makami ya dauka yayi kisa ya tilasta mutane shiga addinin Musulunci, har suna cewa Musulunci addini ne da aka ginashi da kaifin tokobi da zubar da jini

Idan kuna karanta Bible, ku duba surar Karin-Magana (Proverb), zaku ga yadda suka bada tarihin rayuwar Annabi Sulaiman, sun bata tarihinsa, sun bayyanashi a matsayin wani shahararren mutumin banza fasiki mashayi kartagin mazinaci, babu dadin karantawa, to haka turawa suke basu bar Annabawan Allah ba wajen bata tarihi

Kuskure ne babba muna yadda da tarihin da turawa da yahudawa suke rubutawa akan rayuwar Musulmai da kuma Musulunci

Allah Ya bamu ikon gyarawa Amin

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button