Hattara Dai: Saurayi Ya Rushe Maganar Auren Shi Bayan Ganin Bidiyon Tsiraicin Matar Da Zai Aura a Sokoto
Hukumar Hisbah a jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar da kama wasu matasa su uku bisa zarginsu da yaɗa bidiyon wata yarinya da ɗaya daga cikinsu ya yi lalata da ita.
Bayanai sun nuna an saka ranar auren yarinyar a watan gobe, amma sai wanda zai aure ta ya janye bayan da waɗannan matasan da ake zargi suka saki bidiyon a shafukan sadarwa.
Kwamandan hukumar Hisbah Dr. Adamu Bello Asarawa ya shaida wa BBCHausa cewa mahaifiyar yarinyar ce ta kai musu ƙorafi inda ta ce tun a shekarar 2017 matasan suka lalata yarinyar tare da ɗaukar bidiyon.
Dr. Adamu ya ce ”Matashin ya yaudari yarinyar ne ya kai ta otel kuma ya ɗauki bidiyon tsiraicinta. Sai bayan da ta samu miji za ta yi aure sai kawai aka ga ya saki bidiyon.
”Mun binciki yaron ya kuma tabbatar mana cewa abin ya faru, zuwansu otel da abin da ya yi da ita, sannnan mun kamo abokansa biyu da ya turawa kuma su ma sun yi ikirarin cewa shi ya tura musu.”Don haka duk wanda ya samu bidiyon daga baya to ta hanyar abokan nan biyu ya samu,” a cewar kwamandan.
Kwamandan hukumar Hisbah ya ce yaron bai bayar da wasu dalilai da suka sa ya ɗauki bidiyon tare ya yaɗawa ba.”Ɓarna dai ta riga ta faru. Rashin tarbiyya ce irin ta yara.
Ina ga ya yi hakan ne don cin zarafi da lalata mata rayuwa da kuma suna,” in ji Dr Adamu.
Kwamandan ya ce sun tambayi yaron ko zai auri matashiyar ne tun da yanzu ya lalata maganar aurenta, ”sai ya ce min ba shi da niyyar hakan, ai ba zai iya aurenta ba don dama da niyyar yaudara ya je,” in ji shi.
Shekarun yaron 17 ita kuma yarinyar tana da 16 a lokacin da lamarin ya faru. A yanzu kuma yaron na da shekara 20 ita kuma 19 a cewar shugaban Hisbar.
”Dukkansu yara ne lokacin da abin ya faru don ba wanda ya kai 20.”A cewar mahaifiyar yarinyar wadda yanzu aka ce shekarunta kimanin 20, wanda ake zargin ya yi lalata da ‘yar tata ne tun a shekara ta 2017 kuma ya nadi masha’ar ta wayar salula.
Ta ce ya ajiye bidiyon tsawon shekaru uku da nufin wata rana ya yi amfani da shi wajen ɓata sunanta idan yau da gobe ta yi halinta suka ɓaɓe.
”Ni dai a cikin watan Yuni ina zaune yayata ta kira ni daga Legas tana ta salati ta ce ga wance nan ta ganta a bidiyo tsirara ana ta yaɗawa. Sai na kira ƴar tawa na tamabaye ta, sai ta ce min ita ma yanzu take jin labari wajen wata ƴar makarantarsu.”Sai na ce wa take zargi? Sai ta gaya min sunan yaron. Na ce ta ba ni nambarsa. Daga nan na je har gidan iyayensa, na tambayi yaron me ƴata ta yi masa a rayuwa da ya zaɓi yi mata wannan cin mutuncin?” Sai ya ce ba abin da ta yi masa.
Ga yarinya a bidiyon kamar wacce ta sha wani abu ta bugu. Duk wanda ya san tarbiyyar da na yi wa ƴata dole ya taya ni kuka wallahi.”Daga nan sai mahaifiyar yaron ta kira babansa, ta ce ka zo ka ga abin da ɗanka ya aikata.
Daga nan uban ya neme shi da ya nuna mana, sai kuwa yaron ya buɗe bidiyon muka gani.”Uwar yarinyar ta ce bayan haka ne uban yaron ya nemi da a taru a rufawa juna asiri, ”don a ganinsa hakan ba wani abu ba ne,” kamar yadda uwar ta ce.
”Sai ya ce min ai da a ce ciki ne da sai a shiga tashin hankali. Ni ko na ce wannan ma tashin hankali ne. Sai kawai ya ce na je dai kawai.”Ni ko daga can sai na tafi Hisbah na kai ƙararsu.
Da yanzu bikin ƴata 17 ga watan Oktoba ne, amma yaron ya ce ya fasa auren don shi suka fara aika wa bidiyon.”Haka kuwa aka yi in ji rahotanni, bayan yarinya ta yanke shawarar yin aure da wani ba shi ba sai ya saki bidiyon a shafukan sada zumunta abin da ya sa wanda za ta auran ya ce ba da shi ba.
Mahaifiyar wannan yarinya dai ta ce a yanzu haka yarinyar na cikin tsananin damuwa ta yadda ko abinci ba ta ci. ”Ba ta da aiki sai kuka dare da rana.”
A yanzu haka dole mu nemi inda za mu kai ta don ta samu kwanciyar hankali,” a cewar uwar.Mahaifiyar yarinyar ta ce babban burinta shi ne a bi mata hakkin cin zarafin da aka yi wa ƴarta.
Kwamandan Hisbah ya ce za a kai maganar gaban hukumar NAPTIP don ta duba ta ga dokokin da aka tanada kan ɓangaren abin da ya shafi ikirari na saduwa ga masu ƙananan shekaru.
”Su ne ke da hakkin hakan. Sai kuma mu kai hukumar tace bidiyo da fina-finai wato Censor Board don su ma su yi nasu aikin.”Idan sun yi abin da ya dace daga nan kuma sai akai maganar kotu. Kuma abin da ya sa za a haɗa da abokan biyu saboda su nasu laifin shi ne na yaɗa batsar da baɗalar,” a cewar Dr Adamu.
-BBC HAUSA