Muna Tare da Malam nasir el-rufai Bayyani Da Tonon asiri akan Cire Gwman El-rufai A Taron lauyoyin Nigeria~ Datti Assalafy
A lokacin da bakaken yahudawan cikin gida suka sako Musulmi a gaba, to duk lalacewar Musulmin bai kamata a gujeshi ba, balle kuma wanda ba’a da yakinin Musulmi ne lalatacce
Hakika bakaken yahudawa masu ingiza rikicin addinin da na kabilanci a Kudancin Kaduna sun sako Malam Nasir El-Rufai a gaba, sun biya jaridu ana yada batanci a kanshi
Ina da wani bidiyo da na saurari hiran da akayi da Malam Nasir El-Rufai a Channels TV game da rikicin Kaduna, yace shekaru 20 baya kafin ya zama gwamnan Kaduna, masu kunna wutar rikicin addini a kudancin Kaduna malaman addini ne da wasu shugabannin siyasa da na gargajiya
Gwamnan yace Malaman addinin suna cikin voucher da ake biyansu kudi daga asusun gwamnatin jihar Kaduna, idan ba’a biya kudin ba sai su je su tayar da rikici, suna karban kudi har daga kasashen waje a kan wannan rikici na kudancin Kaduna, ni kuma da nazo sai na dakatar, nace ba wanda zai zo na dauki kudi na bashi, laifina kenan a gurinsu
Muna sa ido sosai a kansu, duk wanda muka kammala tattara bayanai a kanshi zamu kai gareshi mu kamashi kowa ye, domin ni bana lamuntar iskanci, kuma ban damu da zagi da batancin da ake min ba, domin ni shugaba ne, inji Malam Nasir El-Rufai
Mun gano cewa hatta cire sunan Malam Nasir El-Rufai da akayi cikin wadanda zasu gabatar da jawabi a gurin taron kungiyar Lauyoyi yana da nasaba da rikicin kudancin Kaduna, sabosa taro ne da zai dauki hankalin duniya, kuma ana tsoron Malam Nasir El-Rufai zai toni asirin masu ingiza ta’addanci a kudancin Kaduna, shiyasa akabi ta bayan fage aka cire sunanshi saboda tsantsar makirci da nuna kiyayya ga Musulunci da Musulmai
To Alhamdulillah, alherin Allah Ya kaiwa kungiyar Lauyoyi reshen jihar Jigawa da kuma Bauchin Yakubu, domin sun fitar da sanarwa sun nesanta kansu da abinda aka yiwa Malam Nasir El-Rufai, kuma sunce ba zasu halarci taron ba
Jama’a ku shaida Muna tare da Malam Nasir El-Rufai dari bisa dari wajen yaki da miyagun Malaman addini da miyagun ‘yan siyasa da suke haddasa rikicin addini a Kudancin Kaduna
Allah Ka kunyata su, Ka tona musu asiri, Ka taimaki Malam Nasir El-Rufai a kan su Amin

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





