Kannywood

Ko Zan Rasa Raina Akanta : Matshin Da Ya sha Guba Akan Maryam Yahaya Ya Sake komawa Kano

Advertisment

Musa Abdullahi, matashin nan mai matukar son ‘yar wasar kwaikwayon Kannywood, Maryama Yahaya, wanda ya sha guba don rashin ganinta ya sake komawa jihar Kano domin cika burinsa.

Daily Trust ta samu zantawa da shi a wannan karonn jin ta bakinsa kan dalilin da yasa ya kusa hallaka kansa don wata ‘yar Fim.

Matashin yace ko kadan bai yi nadamar shan maganan kwari ‘Sniper’ ba saboda bakin cikin rashin ganin jarumar da ya dade yana shaukin gani.

Ban yi nadamar shan guba don ita ba. Nadamar da zan yi shine idan na kasa ganinta.”

Advertisment

Ya ce abokansa da suka bashi masauki a baya sun yi hannun riga da shi saboda tsoron abinda ya aikata a baya.

Shugaban kungiyar yan wasan kwaikwayo na jihar Kano, Malam Alhassan Kwalle, ya ce yaron ne yayi ba daidai ba na rashin sanar da jarumar niyyarsa kafin zuwa Kano da farko.

Lokacin da yaron yazi, bai wurin wanda zai je ya hada shi da Maryam Yahaya ba kuma saboda irin matsalar rashin tsaron da ake ciki, babu mai hankalin da zai bari wani da bai sani ba ya zo ya ganshi.”

“Saboda haka, babu wanda ke shirin kai shi ganin jarumar.” Kwalle yace

Yayinda aka tambayeshi shine ya samu ganinta yanzu da ya dawo, Abdullahi ya ce a’a.

A watan Yuli, Legit ta kawo muku rahoton cewa wani matashi da ya zo daga Yobe ya sha fiya-fiya saboda bai samu ganin Maryam Yahaya ba.

Abdullahi ya yi tattaki tun daga jihar Yobe da ke yankin arewa maso gabas na kasar nan, don ganin jaruma Maryam Yahaya, ya so yayi ajalin kansa saboda rashin cikar burinsa na ganin jarumar ta shi.

Kamar yadda jama’ar da ke wurin suke bayyanawa, matashin ya kwana a Unguwar Zoo road, inda ya zama kamar dandalin taruwar jaruman Kannywood don ya ga jaruma Maryam Yahaya amma bai samu ganin ta ba.

Hakazalika, an ji wasu na cewa sau uku matashin ya yi yunkurin shan fiya-fiya, kafin daga bisani ya bulbulawa cikin sa maganin kashe kwari da ya kusa zama ajalinsa.

An dai samu ceto rayuwar matashin ta hanyar bashi agajin madara.

Sai dai duk da wannan abu da ke faruwa, Jaruma Maryam Yahaya bata san yana yi ba ko kuma ta yuwu bata samu koda labari ba.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button