Labarai
Buruji Kashamu: Cutar korona ‘ta kashe Tsohon Sanatan Najeriya’
Advertisment
Sanata Ben Murray-Bruce ne ya tabbatar da mutuwar abokin nasa a shafinsa na Twitter inda ya ce cutar korona ce ta kashe tsohon sanatan.
A saƙon da ya wallafa, ya ce Sanata Kashamu ya mutu ne a asibitin First Cardiology Consultants, wanda a asibitin ne Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Najeriya Abba Kyari ya mutu.
Kafin mutuwar Sanata Kashamu, ya kasance ɗan majalisar dattijai mai wakiltar Ogun ta gabas.
Ya kuma kasance ɗan takarar gwamna ƙarƙashin jam’iyyar PDP a 2019 a jihar Ogun.jaridar bbchausa na ruwaito.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com