Kannywood

Ina Nadamar Tsinewa kaina a fina-finan Da Na yi a Baya ~ Musa Mai Sana’a

Fitaccen jarumin barkwanci a fina-finan Hausa na Kannywood, Musa Mai Sana’a, ya ce yana matukar nadama a game da tsinewa ko la’antar kansa da ya ke a cikin wasu fina-finansa da ya yi.

A cikin wata tattaunawa da BBC ta Instagram, Mai Sana’a ya ce a da ya yi hakan saboda rashin kwarewa.

Amma a hankali- a hankali sai ya fahimci cewa wannan abu da ya ke fa ba abune mai kyau ba.

Ya ce “Da farko-farkon fina-finai na na yi ta yin abubuwa wadanda ni a ganina dai-dai ne, amma daga bisani bayan da wasu mutane suka ja hankalina a kan abubuwan musamman zagi ko tsinewa kaina da nake, sai na fahimci cewa lallai yakamata na daina”.

Musa Mai Sana’a, ya ce a yanzu ya kara fahimtar abubuwa a fina-finan hausa na Kannywood, kuma ga girma ma da yazo.

Don haka dole wasu abubuwa a jingine su a daina, musamman da ya ke ga shi an fara tara iyali dole a daina wasu abubuwan a cikin fina-finai inji jarumin.

Mai Sana’a ya ce, shi a fina-finansa ana gani kamar yana wuce gona da iri, to sam shi ya ba ya haka.

Ya ce, “Ina yin fina-finai na ne domin nishadi da kuma fadakarwa, kuma na fi yin fina-finai ne ma a kan batun da ya shafi iyaye da ‘ya’yansu“.

Duk abin da aka nayi a cikn fim to fadakarwa nake domin masu irin wannan hali da na yi a ciki fim su dauki darasi su daina inji Mai Sana’a.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button