Labarai

Tun kafa Nijeriya 1914, Ba’a Taba Samun Shugaba Mai Nagarta Irin Buhari Ba —Masari

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari ya jinjinawa gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari Masari kan kokarin da take wajen hidimtawa Nijeriya. Liberty radio na Wallafa

Masari ya ce Nijeriya bata taba samun shugaban kasa kamar Buhari ba tun lokacin da aka kafa kasar a shekarar 1914.

Kalaman na gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, na kunshe cikin wani rahoto da Jaridar, Premium Times ta rawaito, cewa gwamnan ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaba mafi nagarta da Nijeriya ta taba samu ta fuskar samar da gwamnati mai inganci.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a Katsina yayin wani taron gangami da wadanda suka amfana da shirin tallafi na gwamnatin tarayya wato NSIP a jihar suka shirya.

Masari ya ce, shugaba Buhari ya shimfida ginshiki mai nagarta, kuma idan har gwamnatin gaba ta yi amfani da shi yadda ya kamata, yan Nijeriya da dama za su fita daga kangin talauci.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button