Uncategorized
Sa baki a al’aura Na jawo wa mata cuta a Gabansu (Farji)
Sa baki a al’aura mata yau da kullum na jawo wa mata cuta a gabansu da ake kira BV, a wani bincike da mujallar kimiyar lafiya ta PLoS Biology ta wallafa.
BV ba cuta ba ce da ake yaɗawa ta hanyar jima’i. Kwayar cuta ce da yawanci ake samu ta hanyar sa baki a al’aurar mace.
Matan da suke ɗauke da cutar ba za su ji alamomi ba, amma kuma wasu za su dinga ganin ruwa mai wari na fita.
Masu bincike sun gano girman illar cutar da ake ɗauka a baki da yadda take rayuwa ta girma a al’aurar mace.
Game da BV
Kwayar cutar BV ba ta cika yin tsanani ba, amma ya kamata a gaggauta magance cutar da wurin domin samun cutar zai iya haifar wa mata cututtuka da ake samu wurin jima’i da kuma cutar mafitsara.
Idan mace tana da ciki, yana ƙara hatsarin haihuwar ɗan tayi.
Ta ya ake gane an kamu da cutar?
Ba sabon abu ba ne kuma matan da ke ɗauke da cutar za su dinga ganin wani ruwa da yake fita mai wari.
Za a ga sauyin yanayin fitar ruwan kamar zai koma fari-fari da ruwa-ruwa.
Likita zai iya buƙatar a yi gwaji domin tabbatar da idan ana ɗauke da kwayar cutar ta BV.
Idan har aka tabbatar da ana ɗauke da cutar, za a iya magance ta da magunguna ko mai.
Me bincike ya gano?
Matan da ba sa ɗauke da cutar na dauke da wasu kwayoyi masu muhimmanci da ake kira lactobacilli da ke kare gaban mace.
A wasu lokuta wadannan sinadarai na iya raguwa da tasiri ko rage ruwan da ke sa mace ni’ima.
Babu cikakken sani ko bayanai kan me ke haddasa hakan, amma alamomin kamu wa da cutar sun hada:
- Kina yawan jima’i (sai dai matan da basu taba jima’i ba na iya kamuwa da BV)
- Sauyin abokin tarayya
- Kina IUD ( allurar hana daukan ciki)
- Ko kina amfani da turare a kusa ko cikin al’aurar ki
Binciken kimiyar lafiya ta PloS Biology ya nuna yadda alakar cutuka da ake kamuwa a baki ko dadashi ke taimakawa wajen haddasa BV.
Sun yi gwaji a al’aura domin gano yadda wannan cuta take.
Cutar da ake dauka a baki, Fusobacterium nucleatu, na taimakawa wajen habaka sauran cutuka da ke janyo BV.
Masu binciken, Dr Amanda Lewis ta jami’ar California da abokan aikinta, sun ce sun gano yadda amfani da baki a jima’i ke taimaka wa wajen haddasa cutar BV.
Masanan sun fahimci yadda BV ta samo asali daga Jima’i, harda tsakanin mata.
Farfesa Claudia Estcourt, kakakin kungiyar kwararru kan cutukan da ake dauka ta Jima’i da HIV a Burtaniya, ta ce bincike irin wannan na da muhimmanci domin yana fahimtarwa kan cuta irin BV.
”Mun san cewa BV cuta ce mai sarƙaƙiya saboda akwai abubuwa da dama da ke janyo ta.”
Ta ce jima’i ta baki na yada cutuka da ake kamuwa da su ta jima’i da kwayoyin cuta da ke iya lahani ko rashin tasiri ga lafiya.bbchausa na ruwaito
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com