Uncategorized
Kalli Hotuna: An hango sanata Kwankwaso a coci ranar juma’ar data gabata ba bu jar hula
Advertisment
Daga Musa Abdullahi Minista
A ranar juma’ar da ta gabata ne wasu hotunan tsohon gwamnan Kano kuma sanata mai ci, Rabi’u Musa Kwankwaso, suka fantsama a dandalin sada zumunta daban-daban inda aka hange shi a cikin wata Coci ba tare da jar hularsa sanye a kansa ba.
Abu biyu da suka bawa jama’ar dake yawo da hotunan na Kwankwaso a dandalin sada zumunta mamaki sune;
Ganin shi babu jar hula da kowa ya san shi da ita da
Da kuma kasancewarsa a Coci a ranar juma’a da Musulmi ke zuwa masallaci.
Advertisment
Ganin Kwankwaso a Coci ba wani abun mamaki bane idan aka yi la’akari da kasancewarsa shugaba kuma mai burin zama shugaban kasar Najeriya dake da yawan mabiya addinin Kirista.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com