Matsalar Rashin Jin Dadin Saduwa (Jima’i) A Tsakanin Ma’aurata Daga Zauren Fiqhu
TAMBAYA TA 2766
*******************
Assalumu alaikum, Allah ya karawa malam kaifin basira, Malam inaso ka taimaka mun ina neman shawara da mafita a garaka, jiya na cika wata daya da aurena amma wallahi tunda mukayi aure banajin dadin saduwa da matana itama jiya take fadamun cewa batajin dadin saduwa dani, tana yarda danine dan batason sabamun amma wallahi tana sona kuma bata tunanin zata iya rabuwa dani, kuma nima haka nakeji wallahi nafijin dadin na rinka kallonta da ace ina saduwa da ita, dan haka nace Bari na kawo kukana ko zan samu maslaha, na gode.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Shawarata ta farko ita ce ku ziyarci babban asibiti domin ku yiwa likitan bangaren haihuwa (Ganaecologist) bayanin abinda ke damunku. Ina zaton in sha Allahu zaku samu shawarwari daga garesu.
Bayan haka kuma daga cikin abubuwan da zaku kula dasu akwai :
1. Gabatar da wasanni sosai kafin saduwa. Sannan da nuna kulawa da Qauna atsakanin juna (shima yana Qara nishadi atsakanin ma’aurata).
Kada ya zamto baka da lokacin da zaka janyo matarka jikinka kuyi hira ko tattaunawa da juna ko ka sumbaceta atsawon wuni baki daya, sai dai in saduwa zakayi da ita.
2. Abu na biyu idan tana da matsalar ciwon sanyi yana da kyau ku maganceshi domin samun nishadi atsakaninku.
3. Hakanan shafar Aljanu , musamman jinnul ashiq (namijin dare) idan yana tare da mace yakan dauke mata sha’awa, yakan hanata jin dadin jima’i kuma ya sanya mijinta ya kasa samun gamsuwa da ita.
Manyan alamominsa sun hada da ciwon kai, faduwar gaba, mafarkin saduwa, ko firgita, ko kasala wajen yin ibada, da sauransu.
Idan har ciwon sanyin gareku ko shafar Aljanu zaku iya tuntubar Zauren Fiqhu akan wannan lambar domin samun Qarun shawarwari ko magani 07064213990 08163621213.
WALLAHU A’ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (19/06/2020 27/10/1441).




