Uncategorized

Dalilai 10 Da Yasa Mata Ke Bukatar Yawan Saduwa Da Mazajen Su Akai-Akai – Likita MaimunaKwararriyar Likita Maimuna Kadiri ta hori mata da su rika yawan saduwa da mazajen su domin samun annashuwa da karin kafiya a jikin su.

Maimuna wadda ita ce babban likita kuma shugaban kanfanin (Pinnacle Medical Services) ta hori mata da su rika yawan saduwa da mazajen su akai-akai domin samun waraka ga matsalolin rayuwa. Sannan tace hakan na kara kaifin kwa-kwalwar mace.

” A matsayin mu na mata dole ne fa mu rika kusantar mazajen mu matuka ko domin samun lafiyar kwa-kwalwa. Mace kan fada cikin halin damuwa da kakanikayi idan tara samun saduwa da na miji.

” Matan da kan sadu da mazajen su akai-akai sun fi rashin fadawa cikin halin damuwa da matsalolin kiwon lafiya fiye da wadanda ba haka ba. Bayan haka akan samu dankon zumunta tsakanin miji da mata.

Maimuna ta ce mata su dage da saduwa da mazajen su domin hakan ma na warkar da matan dake yawan ciwon kai sannan kuma yakan sa a ji dadin jiki matuka.

1 – Hakan na sa a samu waraka daga yawan yin ciwon kai

2 – Yana kaifafa kwakwalwar mace

3 – Yana kara dankon soyayya a tsakanin masoya

4 – Ya kan yaye damuwa.

5 – Yana kawar da yawan tunane-tunane

6 – Yana gyara jikin mace

7 – Ana samun nagartaccen barci da lafiya

8 – Ana zama cikin farin ciki a ko da yaushe

9 – Fatar mace zata rika sheki da kyaun gani

10 – Yana karkato da ra’ayin namiji ga mace a samu zaman lafiya da so ga juna.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA