Na Kwammace In Kare Rayuwata Ba Tare Da Aure Ba Da In Auri Miji Irin Hakimi -cewar wata budurwa
Tauraron dan wasan kasar Morocco wanda yake taka leda a kungiyar wasa PSG inda ya zamo mutum na farko da yayiwa mata wankin babban bargo ga duk mai tunanin tazo taci banza akan kadororinsa shine yanzu nan jaridar Jakadiya na ruwaito wani labari na wata budurwa a shafin twitter inda take cewa.
Wata matashiya mai suna Zainab Uthman ta bayyana a shafinta na Twitter cewa da ta auri namiji mai halin fitaccen dan wasan kwallon kafa, Achraf Hakimi.
Hakimi dai a yan kwanakin nan ne matarsa ta nemi ya sake ta tare da neman kotu ta umurce shi da ya raba dukiyarsa biyu ya ba ta rabi.
To sai dai kotu da ta yi yi bincike ta gano cewa duk tarin dukiyar Hakimi ya mallake ta ne sunan mahaifiyarsa, wanda hakan ta tayar da kura a kafafen sada zumunta kowa ke tufa albarkacin bakinsa.
Yanzu haka dai wasu matan na ganin cewa ba za su iya auren namiji mai halin dan kwallon ba.