Addini
Sautin Murya :Da Zafinta! Duk Nijeriya Ba Uban Da Ya Isa A Hana Mu Yin Wa’azi ~ Sheik Bello Yabo
Advertisment
Daga Salisu Magaji Fandalla’fih
Babban Malamin Musuluncin nan Malam Bello Yabo, ya ce makirci aka shirya a kama shi da aka yi, amma Allah ya kubutar da shi.
Malamin ya fadi haka ne yayin da yake jawabi ga mabiya a masallacin gidansa.
Malam ya ce ya kamata su sani duk abin da ake yi a duniya na yi don haka ba abin da nake tsoro. Na zauna a gidan yari tsawon shekara biyar, na yi asarar sallar idi 10 a lokacin ina tsare kuma a Sokoto nake ba wani wuri ba”.
Ya ci gaba da cewa ba a yi wa iyalansa da wadanda ke karkashinsa adalci ba domin an hana ya kammala biya musu bukatun Sallah alhali an san an tsara ba za a bar shi ya yi ta a cikinsu ba.
Ya ce “duk Nijeriya ba wanda ya isa ya hana min yin wa’azi domin ita ce hanyar da na zaba.
Na gode Allah ba a kama ni don na yi sata ko neman matar wani ba, sai don na yi wa’azi kuma ba zan bar wa’azi ba har karshen rayuwata”, inji Malam Bello Yabo.
Ya kuma yi godiya ga wadanda yace sun taimaka aka bayar da shi beli musamman shugaban Kungiyar Lauyoyi ta jihar Kaduna da Ministan Shari’a da Shaikh Yusuf Sambo Rigachukun da Shaikh Isah Ali Pantami da Malam Murtala Bello Assada, wanda ya nada a matsayin Sarkin Yakin Bello Yabo a jawabin nasa.
Malamin bai bayyana sunayen wadanda suka yi korafi a kansa ba, sai dai ya ce hukuma ce.
Ga audion nan kuyi Downloading
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com



