Ku San Malamanku tare da Malama Zainab Ja’afar Mahmud Adam
Malamar addinin Musuluncin nan da ke Najeriya, Malama Zainab Mahmud Adam, ta ce mahafinta, marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam ya yi tasiri sosai a kan fafutikarta ta neman ilimi kuma hakan ba ya rasa nasaba da kasancewarta ‘yarsa mace ta farko.
Ta bayyana haka ne a wata hira ta musamman da BBC, a kuma cikin shirinmu na “Ku San Malamanku”.
“Ban sani ba ko don ni kaɗai ce mace a farko tun da misali duk ƴan uwana maza ne a bayana kafin daga baya Allah ya sa aka samu ƴa mace,” in ji ta.
Malama Zainab Mahmud Adam, ta yi karatun nazire a makarantar ‘Yan Dutse daga nan ta tafi makarantar Badar da ke unguwar Ɗan Agundi da ke Kano a Najeriya.
Daga baya a shekarar 1994, lokacin da Alhaji Yusuf Abdullahi ya gina masallaci haɗe da makaranta wato Usman Bin Affan, sai ya miƙa ta a hannun mahaifinta.
Hakan ya sa iyayenta suka koma unguwar Gadon Kaya da ke cikin birnin Kano wadda ta sanya suka koma karatu a makarantar Usman bin Affan, har zuwa matakin sakandare a shekarar 2005.
Ta fara karatun Difiloma a makarantar Legal da ke unguwar Gadon Kaya, amma Allah bai kaddara ta kammala ba sai aka mata aure, ta tafi Madina.
“Kafin kammala Sakandare abubuwa da dama da na karanta na addini sun taimaka min sosai fannin addinin Musulunci. Misali karatun Daura da shaihin malaminmu Malam Dakta Muhammad Sani Rijiyar Lemo a lokacin yana Jami’ar Musulunci ta Madina, idan suka dawo hutu yana shirya Daura wato karatu mai gajeren zango, a markaz dinshi ta Imam Bukhari,” in ji ta.
Ta samu damar halartar karatun kusan kashi uku zuwa huɗu, hakan ya ba ta damar ƙaruwa ta fannin ilimin Islama.
Cikin abubuwan da ke sanyata tunawa da mahaifinta akwai lokutan rubuta jarabawa.
Ta bayyana cewa ba za ta iya tuna yawan kyaututtukan da mahifinta ya ba ta ba.
‘Alƙawarin da mahaifina ya yi mini’
Malama Zainb ta kuma bayyana cewa Aikin Hajjin da ta yi na farko alƙawari ne da mahaifinta ya cika mata na cewa idan ta haddace izifi talatin zai kai ta Makkah, wanda kuma ya cika mata wannan buri nata a 2004 tun kafin ta yi aure.
Ta ce ba za ta iya tuna irin adadin kyaututtukan da yake yi mata ba tun tana yarinya musamman idan ta samu nasara a jarabawa.
Ta bayyana cewa babban abin da ke sawa a yi shiri da mahaifinta shi ne karatu inda ta ce ta yi sa’a kuma Allah ya haɗa ta da miji mai son karatu.
Malama Zainab ta ce wasicin da aminin mahaifinta Sheikh Sani Rijiyar Lemo ya yi mata kan ta dage da karatu a Madina kada ta yi wasa da damar da ta samu ya ƙara ƙarfafa mata gwiwa sosai.
Zuwan Malama Zainab Madina
“Tun da na isa Madina, ba na tsammanin na yi zama ya kai na wata huɗu ba tare da na shiga makaranta ba, na shiga makaranta ta Tahfizul Ƙur’an daban-daban kuma na yi karatu a wani Markaz wanda na yi karatun difloma tsawon shekara biyu wanda Markaz ɗin na da alaƙa da Jami’atul Ɗayyiba ta garin Madina.
“A nan na yi karatu kuma na kammala difloma a 2010 kuma mun ta ƙoƙari domin ganin an samu damar ci gaba da wannan tafiya ta karatu amma kasancewar jami’ar Madina yan ƙasa ne aka fi ba fifiko domin karatu a wajen, hakan ya sa muka yi ta ƙoƙari amma Allah bai nufa ba,” in ji ta.
Ta bayyana cewa a lokacin sai dai Jami’ar ta buƙaci ta yi abin da ake kira distant learning wato karatu daga gida amma a lokacin sai ta ƙi yarda inda take ganin ba karatu bane da za ta samu fa’ida sosai.
Ta ce daga nan sai ta ci gaba da zuwa makarantar hadda wadda take zuwa da yamma a wata makaranta da ke ƙarƙashin jam’iyyar khairiya ta garin Madina inda tana cikin wannan karatu ne sai malamar ajinsu ta yi aure wanda hakan ya sa ta maye gurbin malamar ajin.
Ta ce hakan ne ya sa ta samu wata makaranta da take zuwa da safe domin ci gaba da haddar Al-Ƙur’ani wanda ta ce yinta na daga cikin manyan burikan mahaifinta a kanta.
A makarantar ne ta kammala haddar inda kuma da yamma ta ci gaba da zuwa koyarwa har zuwa shekara biyu da wasu watanni kafin ta koma Najeriya.
“Cikin daliban da muka yi karatu da su a wancan lokacin akwai Dr Hamza Aliyu Sakwaya, Sheikh Khamis Nasidi, Barr Zahra’u Ahmad, Mal Amina Sheikh Barnoma, Mal Fatima Usman da sauransu.
Galibin malaman da suka koyar da mu a wannan makaranta a wancan lokacin kodai malamai ne a Jami’ar Musulunci ta Madina irinsu Farfesa Sheikh Hamad Al Hammad da Farfesa Aliyu Bn Ibrahim Azzahrany.
Ta ce a halin yanzu tana ƙoƙarin kammala digirinta na farko a Jam’iar da ke Kano.
Kusancin Malama Zainab da mahaifinta
“Duk wanda yake da alaƙa ta kusanci da malam ya san yadda muke da kusanci da shi da irin yadda yake nuna ƙauna da tarbiyya da kulawa musamman a gareni.
“Ban sani ba ko don ni kaɗai ce mace a farko tun da misali duk ƴan uwana maza ne a bayana kafin daga baya Allah ya sa aka samu ƴa mace.”
Malama Zainab ta bayyana cewa alaƙarta tsakaninta da mahaifinta ya wuce alaƙa tsakanin uba da ƴa. Ta bayyana cewa rashin mahaifinta ya zama babban giɓi a rayuwarta domin akwai abubuwa da dama da babu wanda zai iya cike mata gurbinsu idan ba shi ba saboda irin kusancin da ke tsakaninsu.
Ta bayyana cewa rashin mahaifinta abu ne da ba za ta taɓa mantawa da shi a rayuwarta ba domin ba ta cika son tana magana a kan lamarin ba saboda har yanzu a wani lokacin tana shiga ɗaki ta kulle ta yi ta kuka saboda a cewarta rashi ne da har ta koma ga Allah ba za ta manta da shi ba.
Burin Malama Zainab
Malama Zainab ta ce tana da buri a kan abin da ya shafi harkar da’awah musamman abin da ya shafi ɓangaren mata.
“Yau ina so na wayi gari na ga Allah ya azurta ni da ilimi mai zurfi da zan yi wa ƴan uwana mata tasiri wurin kawo gyara da sauye-sauye a kan munanan ɗabi’u ko halayya ko rashin tarbiyya a tsakanin mata a kowane mataki na rayuwa,” in ji ta.