Labarai
Sautin Murya : Anzo Wajen Cikin Fushi Sheikh Dahiru Bauchi Yayi Martani Akan Ganin Watan Shawwal 2020
Advertisment
DA DUMIDUNINSA: Sheik Dahiru Bauchi Ya Umarci Mabiyansa Da Su Yi Sallah Yau Asabar Bayan Tabbatar Da Sahihancin Ganin Watan Shawwal
Fiitaccen Malamin Addini, Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya tabbatar da cewa an ga jaririn watar Shawwal, inda ya ayyana cewa yau Asabar ne ranar Idi karama.
Ga yadda sanarwar ta fito daga makusantan Shehin Malamin kamar haka;
“Daga Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi, bayan kammala bincike da tantancewa ya tabbata ‘yan uwa da dama sun ga watan Shawwal. An gani a garin Liman Katagum cikin karamar hukumar Bauchi. Sannan wasu ‘yan uwa sun gani a Zaria har sun sanar da Mai Martaba Sarki.
Dogaro da wadannan hujjoji, Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi r.t.a. ya umarci sauran Almajirai Muridai da sauran jama’a cewa yau Asabar shine 1 ga Watan Shawwal”.
Ga sautin Murya malam ku saurara.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com





