El-Rufai Ya Yi Wa malamai ‘Allah Ya Isa’
Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, Nasir El-Rufa’i, ya yi wa malaman da suka zarge shi da hana jama’a yin sallah ‘Allah-Ya-isa’.
Gwamnan ya bar malaman da Allah ne a jawabin da ya yi ga ‘yan jihar tasa da yammacin Talata.
A cewarsa “Ko a Makka ba za a yi sallar Idi ba, amma mu a nan malamai sun hau mumbari suna cewa mun hana sallah. Kuma sun sani. Saboda haka Allah ya isa.”
Ya ce zai tabbatar babu mutumin da ya shiga jihar Kaduna ranar Sallah daga jihar Kano kasancewar gwamnatin jihar ta Kano ta amince a gudanar da Sallar Idi da Juma’a.
“Ni da kaina zan je hanyar shigowa Kaduna daga Kano na ga mutumin da zai shigo mana. Cuta ta riga ta yi katutu a tsakanin mutane mu kuma mu bari su shigo mana da ita. Ba zai yiwu ba,” in ji Gwamna El-Rufai.
Sabanin wasu jihohi, Gwamna Elrufa’i ya ce kowa ya yi sallar idi da Juma’a a gida domin hana bazuwar cutar korona da ke yi wa duniya barazana.
Har wa yau, gwamnan ya zargi jami’an tsaro da ‘cin amana’ inda ya ce jami’an tsaro na karbar na goro domin barin jama’a su shiga Kaduna.
Gwamna Elrufa’i dai bai fadi lokacin da ake sa ran bude jihar ba, inda mataimakiyarsa ta ce har yanzu basu gamsu da yanayin da cutar take a jihar ba ballantana su bude jihar.
#bbchausa