Uncategorized

Ko Ka San Sinadarin Mayar Da Matarka Ta Ji Babu Kamar Ta A Duniya?

Babu macen da ba ta son mijinta ya rinka ji da ita, yana nuna mata soyayya da girmamawa.

Yin haka na kara wa mace jin ta fi kowace mace ko jin ta samu duniya, sannan duk yarintar mace ko tsufanta tana son mijinta ya rinka daukarta a matsayin ‘yar karamar yarinya.

Ma’ana ya rinka kula da ita kamar yadda zai kula da karamar yarinya, ya rinka tunawa da kuriciyarta da ya sani a da kan ya aure ta.

Saboda haka idan ba ka yin haka, to daga yau ka fara don matarka ta rinka jin ita ma ta kai mace, ta samu farin ciki da jin dadin zaman aure.

 Yin hakan na bayar da kwanciyar hankali a cikin gida, sannan na kara dankon soyayya sosai.

Rinka kula da irin sabon kayayyaki da take sawa ko wani sabon abu da ta canja, kamar yin kitso da kunshi da kwalliya sai ka yaba da nuna birgewa a tare da kai.

Duk wani sabon canji da ka gani yana da kyau ka san da shi, in na yabawa ne ka yaba in kuma na magana ne ka yi wannan shi ne zai kara tabbatar mata da kana damuwa da ita.

Kalmar yarinta ka da ya rabu da bakinka, kamar vebita, ka rinka sawa tana jin a kullum ita ‘yar karamar yarinya ce a gurinka.

Wani lokacin ma ka kira ta da sunan da kamar babanta ko mahaifiyarta suke kiran ta da shi a lokacin da take karamar yarinya, sannan ka fada mata kalaman yabawa masu dadi da cewa tana da kyaun tsari.

Sai kira in ka fita ofis, ka kira matarka duk lokacin da ka kai ofis, sai ka fada mata na kira ne don in tabbatar da jin lafiyarki.

Yin hakan na sa ta san tana da muhimmancin gaske a wurinka sosai.

Wata rana ka ba ta hutun shiga kicin kamar ranar da babu aiki, sai ka shiga ka dafa abincin da za ku ci ko in ba zai yiwu ba sai ka fitar da iyalinka wani wurin birgewar da za su dade suna tunawa.

Zuwa sayayya tare ko zuwa wurin hutu da shakatawa, ka rinka zuwa da ita kamar wata sabuwar budurwarka. Kulawa ta musamman idan tana son yin magana da kai, ka juya ka saurare ta da kyau in kana karatun jarida ko kullum talabijin sai ka rufe, haka in an bugo maka waya kana cikin tattaunawa kar ka dauka ko kuma ka kashe kafin ku fara tattaunawa, ka saurare ta da kunnen basira kamar yadda ka ke yi da in ka je zance.

Sannan ka rinka nuna alamun kana ji da kyau ta alamun girgida kai, murmishi ko amsawa. Sauraren abin da mace ke fada na daya daga cikin abin da ke sawa ta kara girmama ka.

 Ka matso kusa-kusa da ita, kai balle ma lokacin da ka san ta tara gajiya ko lokacin da tana fushi ko take cikin bacin rai, kwantar da ita a kirjinka na iya sawa ta dan huce ko ta samu sauki.

 Ka sa ta ji kamar ‘yar yarinya karama a kirjin ka.

Ka bar ta har ta yi barci daga nan ne za ka gane irin baiwar da Allah ya yi mata da kyau.

Zama a gida ranar da babu aiki don kawai ka kasance tare da ita, sannan ta san kana tare da ita ne ba don kamai ba sai dan kana san ka zauna da ita, ka yi hira, wasanni, maganganun da za su sa ta ji dadin wannan kasancewar da ka yi da ita, domin na sha ganin mata da ba sa son mijinsu yana gida sai in lokacin da zai yi barci.

Yana da kyau wata rana ma ka kulle ta a daki, don kar yara su dame ta, sannan kar ka bar su su shiga har na kamar tsawon awa shida kawai don kana son ta yi barci ta huta, sai kai ka kula da yara na dan wannan lokacin, ka fahimtar da su cewa babarsu na bukatar hutu bari ita ma ta dan ji dadin rayuwarta.

Sai ka yi girki ka kai mata daki ta ci gaba da hutawarta, babu abin da yake sa a ji dadin soyayya face irin wadanna abubuwa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button