Uncategorized

SHAWARWARI 60 GA MATAN AURE | SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

SHAWARWARI 60 GA MATAN AURE

Shawarwari 60 ga matan aure domin samun
zamantakewa mai inganci, da aure mai albarka,
kamar yadda muka Bawa maza suma shawara 60.
1.Ta rike masa amana,
2. Tayi masa biyayya akan duk abinda ba sabon
Allah bane.
3. Ta kula da dukiyarsa
4. Ta kula da Sallah akan lokaci. Da addua zaman
lafiya
5. TA girmama shi a gaban idansa
6. TA kare girmansa a bayan idansa
7. Ta so abinda yake so, koda ba abin so bane a
wajenta
8. Ta ki abinda yake ki, koda ba abin ki bane
awajenta
9. Ta damu da duk abin da ya damu dashi.
10. Ta kau da kai daga abinda ya kauda kai, daga
gareshi
11.Tayi fushi , da dukkan abinda yayi fushi da shi .
12.Ta yarda da duk abinda ya yarda da shi
13.Idan ya bata kadan taga yawansa
14.Idan ya bata da yawa tayi godiya
15.Ta farka daga bacci kafin ya farka
16.Sai yayi bacci kafin tayi
17.Tayi hakuri idan yayi fushi
18 Tayi taushi idan yayi tsauri
19.Ta lallashe shi idan ya hasala
20.kada ta nuna raki a gabansa
21.kada tayi kuka alhali yana dariya
22.kada tayi dariya alhali yana kuka
23.kada ta tsaya kai da fata sai yayi mata wani abu
24.kada ta matsa masa da bukatu
25.kada ta dinka ganinsa kamar yaran gida
26.kada ta dinka yi masa gyara barkatai
27.kada ta dinka kushe tsarinsa
28.Ki dinka zuga shi a gaban danginta
29.Ta dinka girmama shi a wajen kawayenta
30.Ta dinka nuna masa abu mai kyau
31.Ta dinka boye abu mummuna
32.Idan ya kawo wata damuwa gareta, ta taimake
shi ya warware ta
33.Idan ya nuna baya son wani abu ta daina
34.Ta kwantar masa da hankali a lokacin damuwa
35.Ta sassauta masa idan yana cikin bakin ciki
36.Ta tsaya da jinyar sa idan yana rashin lafiya
37.Ta taimake shi lokacin da yake neman taimako
38.Idan yana cikin kunci ta sassauta bukatu
39.Tayi masa rakiya lokacin fita ta tareshi a lokacin
da ya dawo
40.Ta tausasa harshe a lokacin da take magana dashi
41.Ta zama mai tsaftar gida iya iyawarta
42.Ta tsara dakinta sosai yadda zai birge
43.Tayi masa bankwana a lokacin balaguro
44.Tayi ado karshen iyawarta
45.Ta bayyana halaye masu kyau
46.Ishara ta ishi mai hankali ta kula wannan sosai
47.Ta bayyana kanta a matsayin mace
48.Ta iya murmushi da lafazi mai kwantar da rai
49.Ta cika zuciyarsa da sonta idansa da kwalliyarta
50.Tayi kokarin jan hankalinsa da abin da yake so
51.Ta mayar masa da kyakkyawa idan yay i mata
mummuna
52.Ta yafe masa idan ya munana mata
53.Ta karbi uzurinsa
54.kada tayi sallar nafila sai ta sanar masa
55.kada ta dau azumi sai ya sani. 56.kada ta fita daga gida sai ya sani.
57.Ta iya girki kala-kala.
58.kazantar jiki ta dade tana kashe aure a kula.
59.kada ta shigar da wani gidansa sai da izni.
60.kada ta nemi saki ko rabuwa haka kawai
Allah ya zaunar damu lafiya da iyalan mu.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button