Ali Jita Ya samu kambun awardin shekara Daga Tozali Magazine
Fitatcen mawakin Arewa Ali Jita ya samu kambun mawakin shekara daga gidan Jaridar Tozali wanda su ka gudanar a birnin tarayya Abuja tare da karrama wasu mawakan, dattawa, yan siyasa da yan Northflix na ruwaito.
Anyi bikin karramawar ne mai suna Henna Ball & Award Night a dakin taro na international conference center Abuja, ranar Asabar bakwai ga watan shabiyun shakerar nan.
Taron dai ya kunshi abubuwa da dama a ciki kamar al’adun kasar Hausa tare da wasu ababen nishadi da su ka hada fuskokin manyan kasar nan ciki akwai uwar gidan Gwamnan jihar kaduna Hajiya Ummi Nasir Ahmad El-Rufai da kuma uwar gidan gwamnan jihar kebbi Hajiya Dr Zainab Bagudu tare da Gen. kukasheka da kuma dan Majalisar Tarayya Hon Gudaji kazaure, Duk a wajen taron.
An karrama Ali Jita ne da kanbum mawaki mafi tashe na wannan shekara. Ya karbi wannan karramawar ne sakamakon wasu jerin wakokin da ya saki a wannan shekarar wadanda su ka hada da Aboki, Arewa Angel, a sha ruwa, Maryam Gimbiya, Mama da dai sauran su.
An haifi mawakin ne a unguwar gyadi-gyadi da ke birnin Kano a watan Yuli na shekarar 1983. Ya yi karatunsa na firamare da sakandare a makarantar Army Day a tsakanin Jihar Lagos da kuma birnin taraiya Abuja. Ya ci gaba da karatun difuloma a fannin gudanar da aikin gwamnati da kuma kimiyar fasahar sadarwa duk a School for Management Studies da ke garin kano. Mawakin na zaune ne a birnin Kano da mata daya da kuma da daya.
Ali Jiya ya fara sakin wakokinsa a albom ne a shekarar 2009 mai suna Jita. Tun wannan lokacin zuwa yanzu Mawakin ya kasance daya daga cikin jagororin mawakan Hausa a masana’antar finafinai da wakokin Hausa ta Kannywood.
Join Our WhatsApp Channel
Get verified job vacancies, career tips, scholarships and opportunities delivered straight to your phone, free and as soon as they're posted.







