Labarai

Masha Allah : SHEIK SHARIF IBRAHIM SALEH Almajirin Sheik Ibrahim Nyass Da Zai Gina Cibiyar Musulunci Mafi Girma A Duniya (Gidauniya Ta Samu maƙudan Kuɗaɗe )

Daga Dauda Auwal Isah

Shahararren shehin Malamin hadisi na duniya, kuma daya daga cikin jiga-jigan jagororin Darikar Tijjaniyya Almajirin Shehu Ibrahim Inyass a duniya wato Sheikh Shariff Ibrahim Saleh Al Hussainy ya assasa gidauniyar gina katafariyar cibiyar addinin musulunci mafi girma a duniya.

A taron kwanaki biyu da aka shirya, domin assasa gidauniyar bude asusun aikin gina wannan cibiya, an samu halartar manyan baki kamar haka

* Shugaban Kasa Nigeria
* Sarkin Musulmin Nigeria.
* Sheikh Dahiru Usman Bauchi (Rta).
* Cheif Imam Na India
* Sheikhul Islam na Kamaru
* Mufty Na Kasar Ghana.
* Babban Alkalin Libiya.
* Amirul Muminina na Morocco.
* Sheikh Abdulsamad S. Ishaq Rabi’u.
* Sarkin Katsinan Gusau.
* Mataimakin gwamnan Bauchi.
* Gwamnan Sokoto.
* Farfesa Sidi Muhammad Morocco.

Da dimbin Mahalarta taro daga ciki da wajen wannan kasa da baza su lissafu ba.

Wadanda suka sanya hannun jarin su cikin wannan gidauniya da aka assasa,

Shugaban Kasar Nijeriya Muhammadu Buhari shine ya bada filin da za a yi ginin, Sheikh Dahiru Bauchi ya bada naira milyan 25, Farfesa Makary da abokan sa sun bada naira milyan 3
* Gwamnan Yobe ya bada milyan 20
* Gwamnan Sokoto ta bada milyan 40
* Musal Kazeem Bin Sheikh Sharif Saleh ya bada milyan 5
* H. Maryam Sani Abacha, naira milyan 5.
* Gwamnan Borno milyan 10
* Shehun Borno milyan 1
* Alh Dahiru Mangal milyan 25.
* Gidauniyar Dangote milyan 100.
* Kasar Chadi Dala milyan dubu 300 da sefa dubu 200
* Saudiya dala milyan 15
* Kasar Oman Dala Dubu 2
* Kasar Kamaru Miliyan 300
* Saudiya Ta Sake Bada Riyal Dubu 15
* Bola Tinubu Miliyan 25
* Olawiyyo miliyan  5
* Abdul-samad Ishaq Rabi’u miiyan 500 sannan ya bada milyan 50 hadiya ga ruhin mahaifin sa da siminti na naira milyan 500
da sauran wadanda sunayen su bai shigo hannun mu ba.

Za a gina wannan cibiya ne a birnin Abuja.

Muna taya al’ummar Musulmi murnar wannan nasara da Nijeriya ta samu musammam mabiya Darikar Tijjaniya da sauran al’umma.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button