Labarai

Magana sabuwa: Akwai Kurakurai A Ayyukan Hukumar Hisbah – Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya gargadi Hukumar Hisbah ta jihar da ta rika taka-tsan-tsan wajen kiyaye hakkin dan Adam a yayin aiwatar da ayyukanta.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a wani ɓangare na jawaban da ya gabatar yayin ganawa da malamai a Fadar Gwamnatin Kano.

Jaridar Aminiya na ruwaito cewa, Gwamnan wanda ake yi wa lakabi da Abba Gida-Gida, ya bayyana damuwarsa kan wani bidiyo da ya ce ya yi arba da shi kan yadda Hukumar Hisbah ta jihar ke gudanar da ayyukanta wajen kama wadanda ake zargi da aikata laifuka masu nasaba da badala.

A yayin taron wanda Abba Gida-Gida ya yi wa malamai nasihar lura da nauyin da rataya a wuyansu, ya bayyana cewa ya ga wani bidiyo jami’an Hisbah suna cicciba ’yan mata da samari ana dorawa a mota da sunan gyara.

A cewarsa, “Hisbah Hukuma ce mai albarka wadda muka dauka da martaba, kuma muka ɗauko bayin Allah wanda muka san za su iya muka ce ga amanar al’ummar Jihar Kano.

“Amma ma’anar Hukuma shi ne ta yi abin da ya ke daidai kuma a bai wa Gwamnatin shawara sannan a samu hadin kai tsakanin Gwamnati da masu ruwa da tsaki.

“Na ga wani bidiyo da ya tayar min da hankali, kira nake da jan hankali gyara muke so.

“An ɗebi motoci, an je inda wasu matasa ke ɓarna maza da mata, amma yadda aka riƙa debo su ana duka da gora, suna gudu ana bi, ana tadile kafafunsu, ana debo su kamar awaki haka a jefa su a cikin Hilux.

“Wani ma Allah Ya kiyaye in kashin bayansa Spinal Cord ya karye ya gama yawo har abada.

“Wannan muna ganin kuskure ne babba, ka rungumo matashiya ko matashi ka jefa shi kamar akuya a cikin Hilux.

“Na ga bidiyo da aka je inda ɗaliba a Jami’ar Bayero suke har inda suke har dakunansu ana duka ana rungumosu, ana jefa su a cikin mota.

“Mu muna ganin akwai gyara. Mun saka hukuma saboda ta yi wa addini musulunci hidima, amma idan aan irin wannan to yaran ma sai su kangare, abin da ake so su yi na gyaran sai a samu akasin haka. Allah Ya kiyaye.

“Idan yaran nan suka kangare mana a Jihar Kano, yaya za mu yi da su? Amma a fita da motoci, a fita da jami’an tsaro, a hada da Hisbah, a hada da ’yan sanda, a hada da Sibil Difens, amma ba ma so a hada da sojoji, don idan aka hada da soja ta baci.

“A je da SS, duk inda aka san ana wannan aiki marar kyau, a je a kamo wadannan yara ko wadannan mutane a danka su a hannnun hukuma, don Allah Yana son ka kare mutuncin dan Adam dan uwanka,” inji Gwamnan.

-Aminiya

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button