Bidiyon yaro tsaye cak kan mazaunan mahaifiyarsa yayin da take tafiya ya dauki hankula
An ga bidiyon wani yaro tsaye cak a mazaunan mahaifiyatsa yayin da take tafe shi kuma yana kwasar nishadi da yin hakan, Yen.com.gh ta ruwaito.
A bidiyon wanda hankulan jama’a da dama ya karkata akai, an ka matar tana tafea titi ba tare da dagewa ko kuma daure yaron da zani a bayanta.
Matar ta ci gaba da tafiyarta ba tare da damuwa ba kasancewar ta san babu matsala kuma ba zai fado daga wurin ba.
Bidiyon wanda wanda ya ga matar da dan ta ya dauka ya janyo mutane da dama su na yabon surar matar inda su ke cewa Ubangiji ya yi mata baiwa.
Wannan dalilin ne ya sanya su ka dauki bidiyon don su nuna wa ma’abota amfani da kafafen sada zumunta.
Sai dai abinda zai ba mai karatu mamaki shi ne yadda kowa yake tafe ba tare da mayar da hankalinsa kan ta ba, kamar abinda aka saba gani.