Jerin kyawawan matan ‘yan siyasa Guda hudu Na kasar nan
Legit.ng ta tsakulo muku jerin matan ‘manyan ‘yan siyasa kyawawa guda hudu a kasar nan
A Najeriya shiga harkar siyasa ba karamin abu bane, domin siyasa a Najeriya abu ce mai hatsarin gaske, sai wadanda suka cika suka batse suke shiga harkar siyasa a Najeriya. Duk macen da ta auri dan siyasa a Najeriya ana yi mata kallon wacce Allah ya albarkaci rayuwarta, domin ana yi mata kallon wata mace ta dabanne.
Wannan karfin mulkin yana zama wani abu a garesu, domin nauyi yakan karu a kansu, domin sune suke da alhakin jagorantar mata wurin ganin an kawo cigaba ga al’umma.
Hakan ne yasa matsayin ‘First Lady’ yake da matukar muhimmanci. Ana bukatar mace mai kyau, mai ilimi, da basira. Hakan ne yasa zaku ga ba kowacce mace ke iya taka wannan matsayin ba.
Legit.ng ta tsakulo muku jerin matan ‘manyan ‘yan siyasa kyawawa guda hudu.
1. Precious Fani Kayode
Allah ya albarkace ta da kyakkyawar fata, ga kyau tamkar ita tayi kanta, bayan haka kuma Allah ya ba ta basira da ilimi.
Ta auri tsohon ministan jiragen sama, kuma babban dan siyasa a kasar nan, Femi Fani Kayode, Precious mai shekaru 30 tana da yara guda hudu, kuma har yanzu jikinta yana nan tamkar na yarinya.
A shekarar 2007, Precious ta lashe gasar macen da tafi kowacce kyau a Najeriya. Sannan kuma an zabeta ta wakilci Najeriya a taron kyawawan mata da aka yi a kasar Jamaica a shekarar 2014.

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)













