Labarai

Hanyoyin Magance Yawan Gumi,Tsami Da Warin Hammata

Gumi (Perspiration) na daya daga cikin hanyoyin da jiki yake bi wurin rage zafi (heat) da fata ke fitarwa.

Hallitun glands da ake dasu a jiki na fata sune suke fitar dashi.

Ko wanne sashen jikin dan adam na dauke da qwayoyin halittar microorganisms da ake ce musu normal flora ma’ana wadanda basa cutar da mutane sai dai ma taimakawa.

Su wadannan microorganisms wadanda ake samu a jikin dan adam musamman hammata, idan suka hadu da gumi shine ake samun chemical reaction tsakanin su sai su mayar da gumin yanayin wari na daban shine ake samun warin hammata da jiki.

Akwai yanayin bambamcin halitta da yake sawa wasu sunfi wasu yawan gumi sakamakon yanayin yadda glands din su yake aikin fitar da ruwan gumi.

Dalilin da suka sa yawan gumi akwai :-

-Yanayin bambamcin halitta domin maza sunfi yawan gumi sama da mata.

-Yanayin sana’ah ga masu aikin qarfi da masu yawan shiga cikin cunkoson jama’ah.

-Aikin motsa jiki kamar guje-guje da makamantansu.

-A bangare guda kuma larura ko rashin lafiya kan iya haifarrwa da mutum yawan gumi kamar ciwon siga da sauran su.

Cikin hanyoyin da mutum zaibi domin rage yawan gumin da yake akwai :-

-Aske gashin hammata da qasan mara.

-Wanka da tsaftar jiki

-Tsaftar kayan da ake sawa kafin dora sutura Boxer,singlet ga maza Bra da Pant ga mata ta hanyar wankesu da canjawa kullum.

Idan an saka kaya ko da datti bai bayyana ba ayi qoqarin wankesu kafin kuma sakawa saboda warin gumin hammata da jiki.

-Amfani da Deodorant da Antiperspirant (Roll on da Body spray) ga wanda Allah ya horewa.

-Idan babu sarari amfani da Alimun ya wadatar ko da babu turaren jiki.

-Ga wanda Allah ya horewa amfani da sabulu mai qamshi lokacin wanka shima yanada kyau Idan kuma ba sarari duk wanda Allah ya hore ayi amfani dashi.
Abunda akafi buqata shine wankan.

Ga wadanda kuma gumin nasu yayi yawan gaske, yanada kyau a ziyarci asibiti bangaren Endocrinologist domin ta iya yiwuwa akwai larurar da take haddasa yawan hakan.

©✍️Amb(Nr) Sumayya Ibrahim Sa’ad
RN,RM,PND

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button