Kannywood

Wata sabuwa ! Shahararren Darakta Abdulmumin Ilyasu Tantiri Ya Fice Daga Kannywood

Advertisment

Fitaccen jarumi kuma mai bada Umarni Iliyasu Abdulmumini wanda ake yi lakabi da ‘Tantiri’ ya bayyana cewa ya fita daga  cikin masana’antar shirya Finafinan Hausa, saboda rashin gamsuwa da shugaban na masana’antar. Tantiri ya bayyana ficewar sa ne a shafin sa na Instagram. Ga abin da ya rubuta @abdul_ilyas_tantiri :

“Assalamu alaikum,Ni ABDULMUMIN ILYASU MAISANGO ina sanar da ficewata daga cikin masana’antar KANNYWOOD Saboda Rashin gamsuwa da shugabancin wannan masana’anta baki daya,tareda wasu dalilai da suka shafeni.Bissalam NAGODE.”

Kafin ficewar sa dai, jarumin yana daya daga cikin jaruman da suka fara suna a masana’antar Fim tun farkon kafata. Sannan ya bada gaggarumar gudummuwa a harkar, ya kuma shirya tare da bada umarnin manyan Finafinai.

Advertisment

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button