Uncategorized

Nasihar Wata Uwa Mai Hankali Ga ‘Yarta Yayin Aurenta

1 – Ki zama kamar baiwa ga mijinki, sai shima ya zama kamar bawa a gare ki.

2 – Kada ki nisance shi, sai ya manta dake.

3 – Ki kiyaye masa hancin sa,jinsa, da ganinsa; kada ya shaki wani abu daga gareki sai
mai qamshi kada yaji wani abu daga bakinki sai mai dadi kada yaga wani abu daga gareki sai mai kyau.

4 – Ki kiyaye masa lokacin Abincin sa da lokacin Baccin sa, domin yunwa tana hassala mutum, kuma gurbata masa bacci na fusata shi.

5 – Ki kiyaye masa Dukiyar sa,dangin sa da gidan sa, domin suna da matukar muhimmanci a gareshi.

6 – Ki guji yin farin ciki yayin da yake cikin bacin rai, kuma ki kiyayi yin bakin ciki, yayin da yake farin ciki.

7 – Ki girmama shi matuqa shima zai girmamaki matuqa, fiye da yadda kowa zai girmamaki.

8 – Ki sani cewa gwargwadon yadda kike amincewa da ra’ayin sa gwargwadon tausayawar da zai miki.

9 – Kada ki juya masa baya yayin da ya kusanto gareki.

10 – Ki sani yake ‘yata baza ki sami yadda kike soba har sai
kin zabi yardar sa akan yardar ki, kin fifita son ransa akan son ranki.

11 – Kada ki fiya naci ko fushi a lokacin da kike neman wani abu agareshi, sai ya kosa dake.

12 – Daga karshe don girman Allah ki yi hakuri ki zamo shimfida ga mijinki zai zamo rumfa a gareki.

ALLAH YASA SAURAN YAN UWA MATA SUMA SUYI AMFANI DAWAN NAN NASIHA.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button