Kannywood
Banda gashin kaina dake bude: Kayannan dana saka basu sabawa shari’aba, zan ma iya yin Sallah a haka -Ummi Zeezee
Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta yi wani jawabi a shafinta na sada zumunta inda tace, daya daga cikin kalubalen da mutum ke fuskanta shine tarin makiya
Ta kara da cewa saidai makiyine kawai zai yi maka gyara a lokacin da ka aikata ba daidai ba.
Ummi tace amma matsalar shine idan aka tashi yin gyara sai a rika yiwa mutum ta yadda bazai dauka ba maimakon a yi cikin Nasiha.
Wasu mabiyan Ummin sun jawo hankalinta akan kayan data saka a wannan hoton inda sukace be dace ba ta daina.
Saidai ummi tace kayan nata basu sabawa shari’a ba in banda gashin kanta da ta bari a bude kuma tana samun babban mayafi ya rufeshi tsaf zata iyayin sallah a haka.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com