Kannywood

Rabon kudin Kamfen ya tada kura tsakanin Ummi Zeezee da wasu manyan yan wasa

Tsohuwar ‘yar wasan fina-finan Hausa da ta yi fice wajen bayyana kusancin ta da tsohon shugaban Kasa Ibrahim Babangida da dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ta aika wa wasu daga cikin abokan aikin ta kwando-kwando na ashar tare da barazanar sa a rufe mata su a Abuja.

Ummi Zeezee ta koka ne cewa Atiku Abubakar ya aiko wa magoya bayan sa da ke farfajiyar finafinan Hausa da kudade masu yawa inda suka ware kan su sannan suka raba kudin ba tare da sun aika mata da kaso mai tsoka ba.
A shifidaddiyar wasika da ta rubuta inda ta jero sunayen wadanda take yi wa raddi da sakon nata ta ce dukkan su sunci sa’ar mahaifiyar ta ce da ta roke ta da ta yi hakuri da yanzu Sani Danja, Fati Muhammed, Zaharaddeen Sani, Alamin Buhari da Darakta Emrana sun dade a garkame a ofishin SSS na Abuja.

Ga yadda wasikar ta zo: kamar yadda ta wallafa a shafinta na Instagram: “Zuwa ga Fati Mohd, Sani Danja, Zaharaddeen Sani, Al’amin Buhari and director eemrana….

”A ranar JUMA’AR data gabata mai girma dan takaran shugaban kasa ta jam’iyar PDP Alhaji atiku Abubakar ya shirya wani taro da zaiyi da yan fim da kuma mawaka na kannywood dan gane da siyasarsa sai dai kuma Allah bai bashi ikon zuwa ba sai ya wakilta sir Bukola Saraki Wanda daya zo taron ya bada kyautan makudan kudi miliyoyi ga jarumai da kuma mawakan kannywood Wanda suke PDP suke kuma yiwa wazirin adamawa kamfen.
“Ammah sai gashi saboda son zuciya irin taku kuda na lissafo sunayenku kuka raba kudin a iya tsakaninku kawai ko wanne acikinku ya dau naira million hudu da rabi saboda zalinci tsantsa.
”To shi ai Bukola Sarakin ba ku kadai ya bawa kudin ba da zaku rabashi kawai a tsakanin ku shi cewa yayi ya bayar ga duk yan PDP na kannywood masu yin atiku wai ammah sai kuka fara kawo uzurin karya cewar wai acikinku ko wani mutum ya gaiyato mutum hamsin ne domin taron shiyasa kuka raba kudin a tsakaninku Wanda kuma karya ne ba wasu mutane hamsin hamsin da kuka kawo taron domin nima na je taron kuma a matsayina na babbar yar PDP mai manyan mukamai har biyu baku bani nawa kudin ba.
”Sai bayan an tashi daga taron ne na kira actor zaharaddeen sani awaya ina tambayar nawa kudin wai shine dan renin hankali ya aikomin da naira dubu 250k kawai sai kace ya daukeni yar jagaliyar siyasa koko ince ya daukeni matsiyaciya ko yar yunwa.
“Dan haka wannan wasika na muku ne domin in muku gargadi.“Wallahi wallahi wallahi in aka sake hada taron daya shafi atiku abubakar kuka raba kudi bani aciki to duk sai na kulleku a DSS na abuja baza a barku ba har sai kun biyani kudina domin na tabbatar acikinku ba mai connection din da nake dashi a Nigeria kuma ko wannan kudin ma dakuka dannemin rabo na naso na rufeku duka shine danayiwa mamana waya na gayamata ta hanani tace rigima ba dadi in barku da Allah kawai zai sakamin shiyasa na rabu daku bawai dan ina tsoronku ba domin naga sauran mutanen da sukaje taron kuka hanasu hakkinsu tsoro ya hanasu magana.
”Dan haka acikinku in akwai dan iska to dan allah in an sake bada kyautan kudi akan siyasar atiku mutum yaci nawa yaga mezaifaru!macutan banza kawai!!”

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button