Uncategorized

IZNAH PART 7 : Labari Cike Da Makirci

IZNAH *7*
Ahankali baffa ya ‘dago ya kalli yanda take aikin cikin sanyin jiki duk saiyaji qaunar yarsa da tausayinta Dana yaron ya qara shigarsa ya bu’de baki ahankali yace,
Zo Nan Anano.
‘dauraye hannayenta tayi ta taso ahankali ta zauna kusadashi ya kalleta dakyau yace,
Anano bazamu bar yaron nanba a gidan Nan sbd mumaganganun dake yawo zasu Bata Miki suna su Bata Mana zuria shiyasa na yanke shawarar Yusuf da Usman zasu kaisa binni gidan marayu…..
Kaka tasake ahankali batareda yakai qarshen zancen nasaba.
Shiru yayi Yana sauraron kukan nata ganin batada niyar dainawa yasa ya dafa kanta yakira sunanta.
Bata ‘dagoba saidai tadan tsagaida da kukan.
Cikin tsananin qaunarta dake rinjayarsa kowane lokaci yace,
Anano wlh da inada wani zabin bayan wannan da bazan rabaki da ‘dannan ba sbd koba komai mun taimakesa Kuma bamusan baiwar da Allah 6oye cikin alamarinba saidai vanida wani zabin kodan gudun lalacewar sunanki.
Cikin kuka ahankali tace,
Baffa Dan Allah karka biyewa maganar mutane ka fasa abinda kayi niyya na taimakawa marayan Allah dabaisan kansaba.
A qule Yusuf yace,
Ke dallah ki rufe Mana shegen bakinki badan shegen iyayinki da rawar kanki ba da duk haka Bata faruba,
Wannan yaron yagama barin gidannan Dan wlh bazai zaunaba.
Cikin takaici Aliyu ya kar6e zancen da cewa,
Wama yasani ko shegene uwar tasa ta Haifa.
Katsesu baffa yayi da cewa,
Koma dai meyene shi yaron bayada laifi tako Ina Kuma kamar yanda Anano tace munyi niyar taimakawa sabida Allah Kuma zamuyi.
Tunda suka fara magana Inna ko inda suke Bata kallaba sai lokacin takallesa cikeda mamakinsa tace,
To yanxu abinda takeson shi kake nufin za’ayi kome?
Eh”’yafada Kai tsaye tareda kallon jafar da tuni jaririn ke hannunsa Yana ‘dan jijjigasa sbd dagashi Sai Anano ke saukarsa a gidan Sai Inna idan zatai Masa wanka Amma ko baffa Sam bai ta6a daukarsaba iyakaci dai Yana tausayinsa shima sbd ananonsa nasonsane kawai.
Cikin sakewar fuska yace,
Jafar meye shawararka akan hakan?
Kallon yaron yayi yakuma kalli Anano datai zuru cikin hawaye Sai yaji tausanta da ‘dan yakalli baffa yace,
Baffa shawarata ‘dayace
Komai zakayi kayisane domin Allah badan waniba kokuma badan abinda wani zai fa’daba..
Murmushin qarfin hali baffa yasaki cikin jinjina Kai yace,
Usman da jafar ku shirya zuwa jibi zamukai Anano gurin gwaggwonta tareda yaron zuwa wani lokaci idan komai ya lafa saita dawo.
Ajiyar zuciya Inna ta sauke duk dai bahaka tasoba tasone su yarda qwallon mangwaro su huta da quda Amma ko ahakan da sauki sbd itadai dama damuwarta zaman yaron ne agidan bataso ga ananon da shegen taurin Kan tsiya sbd samun daurin gindi daga baffan.
Yusuf da aliyu kuwa miqewa sukai suka ficewarsu sbd takaicin hukuncin da baffan yanke na barin yaron.
Anano kuwa jikinta ne yayi sanyi ta matsa ta riqo hannun baffan ta kallesa hawaye na gangaro Mata tace,
Baffa Allah zai saka maka da mafificin abinda kayi Koda a bayan ranka ne.
Shafa kanta yayi yace,
Allah yabiyani ta hanyar kawo farin ciki da haske Mai dorewa a rayuwarki ananona.
Jafar ne ya katse yanayin nasu na shaukin uba da ‘ya ta hanyar cewa,
Yaron haryanxu bashida suna..
Fuskar Anano baffa ya kalla yace,
Anano za6ar Masa suna.
Sunkuyar dakai tayi cikin fargaba tace,
Abdulshakur..
Su Inna sunaji suna gani baffa yasa jafar ya Kama rago ‘daya ya yanke aka ra’dawa yaron suna abinma Sai ya daina Basu takaici sbd ganin yanxu Kam su baffa kawai wahalar ta fasha sukam sun cire hannunsu musamman aliyu daya tsani Koda ganin yaron.
Kafin jibi ranar tafiyar tayi gata da kulawa sosai baffa da jafar suka shiga nuna Mata harma da Usman yanxu da ananon ke basa tausayin ganin Allah ya ‘dauki son abinda batada alaqa dashi yasa Mata kamar jininta saiyake ganin hakan da wani 6oyayyan sirri daga Allah.
Ranar dazasu tafi sosai tayi kuka kamar ta tafi kenan musamman dataga Inna na farin ciki da tafiyar tasu Dan har Allah Allah take su wuce.
Basu shiga motar mandeba sbd gudun tsegumi Kai tsaye doguwar tafiya sukai da qafa har bakin babban titi kafin suka shiga motar shiga yola.
Tunda suka iso taji hankalinta yafara tashi Dan hakanan takejin fa’duwar gaba.
Direct wata qaramar unguwar talakawa suka nufa cikin adaidaita jafar dayasan gidan Yana nunawa Mai napep ‘din inda zaibi.
Har bakin kwanar layin gidan aka ajesu Nan baffa ya biyasa suka gangara suka shige lungun.
Ba wata tafiya sukaiba suka iso gidan jafar ne agaba Yana kwada sallama suna shiga Dan qaramin tsakar gidan asiya matar qanin mijin gwaggon daya rasu ta fito ‘dakinta tana Sanya hijab tana ganin jafar ta washe baki tana musu sannu da zuwa tareda ‘dauko musu tabarma tana cewa,
Gashi kuwa gwaggon batanan tanacan gidan datake aiki rasuwa akai musu matar gidance ta rasu gurin haihuwa.
Allah sarki Allah yaji qanta….cewar jafar dake qoqarin juyawa waje yafadawa baffa da Usman gwaggon batanan.
Kallon hijabin anano asiya tayi ganin Sai muqu muqu take batason asan meyene aciki tace,
Ananon gwaggo bazaki zaunaba.
Qoqarin zaman take jafar yasake shigowa Yana kallon asiya yace,
To Wai zamu samu Wanda yasan can gidan da gwaggon take Sai akaimu?
Eh Bari nakira Bello yananan waje saiya kaiku yasan gidan.
Qofar gidan ta nufa saidata gaisadasu baffa kafin ta kirawo bellon a gidan maqwaftansu inda suke kallon qwallo ‘dakin abokinsu.
Sallama sukai Mata suka nufi titi Bello Kam Yana tare Mai adaidaita kwatancen gidan yayi Masa Dan shikam baiso ya rasa kallon qwallonsa Dan yau wasar na zafi sosai.
Yana fara kwatancen Mai adaidaita yace ya gane sbd gidan ba wani a boye yakeba idan kaje anguwar danma masu adaidaita da mashin Sam basa shiga layin Dan mugayen soldiers din dakecin uwarsu na gadin gidan.
Nesa ka’dan da gidan ya tsaya ya nuna musu gidan da hannu suka biyasa ya juya suka nufi gidan kowannensu gabansa na ‘dan tsinkewa sbd ganin gidan da akace nanne ga sojoji dasuke hangowa tun daga nesa.
Wangale qaton gate din sukaga anyi wasu jibga jibgan motoci suka fito aguje kamar zasu tashi sama ta qarshen ita ta tsaya sauran sojojin dake qofar gidan suka fa’da ciki aka figa da qarfi harsaida su baffa suka daka wani mugun tsalle suka ra6e gabansu na qarasa tsinkewa Dan Anano tuni taji ta tsinke tana adduar Allah yasa ba anan gwaggon zata zauna da itaba sbd Allah yagani arayuwarta ba abinda ta tsana take tsoro irin soldier.
Baffa ma Kam wani irin mugun yawu ya ha’diye na tsoro da tausayin ananon Dan shima Kam Yana tsoron kaki( kunsan Fulani da tsoron soja?? just kidding)
Usman damashi tuntuni atsure yake tunda suka iso yaga mutane sunyi Masa yawa Dan harwani jiri jiri yake gani Dan baita6a fitowa birni duk cikinsu jafar ne kawai Mai zuwa shima sbd visiting din ananon ne idan tana makaranta.
A darare suka Isa bakin gate din kusan atare suka ‘dan sauke ajiyar zuciya ganin ba soja ko ‘daya days saura.
Cikin Yar fargaba jafar ya qwanqwasa qaramar qofar qatoton gate din dayake jabiru na kusa Yana hamdalar samun yancin aikinsa oga saheeb Yakoma da gayyar sojojinsa.
Bu’de qofar yayi Yana ganinsu ya fito tareda jawo qofar Yana kallonsu a ‘dage sbd daka gansu kaga fulanin qauye futuk ananon cema ta’dan banbanta ka’dan acikinsu.
Ganin irin kallon dayake musune yasa jafar jiki amace yace,
Dan Allah gwaggo hinde muke nema.
Sake kallonsu yayi dakyau kafin yace,
Wa za’a cemata sunxo?
Kacemata baffa salisu ne yayanta daga qauye tareda Anano.
Juyawa yayi yashige tareda maqala sakata ya nufi babban part ‘din oga saheeb.
Zag
ayawa yayi ta qofar baya inda ‘dan qaramin boys quarter din part dinsa Wanda ke ‘daukeda Palo ‘daya da room daya Sai toilet.
Ta qofar kicin din part dinsa zaka it’s fadawa direct palon gwaggon Wanda anyi hakan ne Dan aikinta basaita zagayo ta qofar paloba Kuma nafeesa ce tasa akai Mata hakan sbd tsananin qaunarta da gwaggon hakama shima saheeb sosai Allah yasa Masa qaunar gwaggon da ganin girmanta.
Qwanqwasa qofar palon zaiyi saigata ta fito zataje can 6angarensu mum asee.
Da mamaki take kallonsa tace,
Mal jabiru lafiya naganka nan….
Baqi kikayi sunce baffa salisu da anono ne koma meye sunan na manta….
Da sauri ta nufi gate din cikin farin ciki dakuma fargabar Allah yasa lafiya wannan zuwa haka.
Shigo dasu tayi har cikin boys quarter palonta inda baffa daqyar ya zauna takawo musu ruwa suka gaggaisa baffa yace,
Dagacan muke gidanki aka kawo mu Nan.
To hamma salisu Allah dai yasa lafiya.
Anano ya nuna Mata ta waigo Sai alokacin ta lurada ‘da ahannunta.
Zaro idanuwa tayi tana sake kallawa danta gasgata idanuwanta tace,
Na boni ni hindatu menene wannan ahannunki Anano.
Ba yanda kike tunani bane Nan dai yayi Mata bayanin komai ya ‘dora dacewa,
Nakawota da kainane danta zauna agurinki idan komai ya lafa saita dawo.
Badan zuciyarta tagama aminta da zancen ‘dan bana Anano bane jiki amace tace,
To shikenan zanyi magana da Mai gidan idan ya amince saimu zauna anan idan bai aminceba zamu koma gida Dan dama jiya da’akai kwana bakwai da rasuwar Mai ‘dakinsa naso tafiya yace nayi zamana anan harsai yace na tafi.
Ba yanda bataiba dasu su tsaya suci abinci sukaqi musamman Usman da yake a firgice kamar ace qyat ya ruga da gudu.
Har titi suka rakasu suka tafi Anano da baffanta kamar karsu rabu musamman dayaga tana kuka ahankali.
Tundaga gida dama gwaggo ta kar6e ‘dan tagoyasa shiyasa Koda suka juyo ananon ke tafiya ahankali tana share hawaye jitake kamar karta koma gidan.
Suna shigowa direct part din mum asee suka nufa Dan Inna ta gabatarda ananon daidai zasu shiga Kamal shikuma yafito cikin sauri zai fita saiji yai yayi karo da mutum ba zato.
Please ku ringa saurarawa kuga menene zai faru kafin ku ringa magana akan abinda yadace da Wanda bai daceba afterall karku manta novel ne is not reality so Dole wasu abubuwan zasu banbanta da reality so please take note#no bad comments ko Kuma judgen abinda bakusan qarshensa ba Dan bakusan me writer ta shirya rubutawa agaba ba.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button