Uncategorized

Gyaran Fuska Tayi Haske Ba Tare Da Anyi Amfani Da Chemical

Gyaran fuska tayi fari da sheki naturally batare da kinsa chemical a fuskarki ba. Sannan zanyi bayani akan matan da suke tsintar kansu da wani irin wari ko kuma wani baki-baki a cikin armpit dinsu(hammatarsu) ko bakin fuska daga gefe daya due to bleaching products or sunborn. Dafarko idan kika ga fuskarki na irin wannan duhun daga gefe ko kusa da idonki to cikin biyune kina shafa cream kina shiga rana ko kina shafawa lokacin gari da zafi. Na biyu ko kina shafa man dayafi karfin fatarki to dai koma menene ya janyo ga hanyar da xakibi ki goge wannan tabo zaki sami madara ta ruwa kisata a fridge tayi sanyi sosai sai ki goga a wannan tabon naki bayan minti ashirin saiki wanke sannan idan gari da zafi zaki sami ruwan sanyi kisa cottonballs ki tsoma ki dora akan tabon saiki bari yayi minti 5 saiki cire cotton din ki shafa mai a fuskar.I dan kika yi sau uku saiki dinga yiwa fuskar gaba daya.Am assuring you zaki mamaki sosai. WARIN HAMATA-waddata sami kanta da irin wannan warin ko bakin saita sami bakin soda tasa lemon tsami daya ta kwabata tashafa a hammatar har minti goma sha biyar sannan ta wanke intanayi kafinta shiga wanka zataga komai ya daidaita. NATURAL FACE WHITE- Idan kinaso fuskarki tayi fari batare da side effect ba saiki sami cinnamon powder da paste na gwanda ko kabewa da olive oil kadan kishafa a fuskarki kafin kishiga wanka insha Allahu inkika juriyin wannan fuskarki zata dinga fari kamar me bleeching..

 Sabulun gyaran fata,salaushinsa dakuma maganin tabo

 Kisamu sabulun salo,wato ghana soap,kisami madara,leman tsami dakuma kurkur da haska amarya,kisamu sabulun broonze bashida tsada ana saidashi a irinsu sahad,departmental stores haka saikuyi kokari kunemi sabulun caramel shima duk acikin kayan hadine to kisamu kihada sabulun duka ki daddakasu kokuma ki yanyankasu siri siri saiki gwamutsasu sannan saikikawo kurkur daidai misali ki juye kisamu haska amarya daidai misali shima ki juye.haska amarya da kurkur agidagen gyaran jiki ake samunshi saikihadeshi asabulun kibuge sannan wasu sunasa nescafe domin yanasan laushin fata inkinaso kisaka inbakyaso saiki barshi saikijuye madararki ki buga saikikawo ruwan leman tsaminki dakika matse shima ki juye,idan kikai hakan saiki bugesu sosai su hade,zakiga yayi ruwa ruwa amman ba komai bane,saiki juye wannan hadin cikin container mai murfi ki rinka wanka dashi wannan hadin yanamugun gyara fata,ba bleaching yakeyiba,gyarafata yake yanakuma maganin kujaren fata dakuma kurajen fuska yana mugun gyaran jiki sosai kuma yanada kyau ku rinka shafa sabulunnan kamar anasaura awa daya kiyi wanka yanadakyauma kisamu ganyen magariya busasshe ki daka kizuba akan sabulun dakika hada kikara bugewa bakaramin kyau zakiba duk tabon dake jikinki saikinnema kinrasasu mata ayi kokari agyara fata dan miji yakalla yaji dadi yanasa tsansin fata dakuma laushinsa.

Gyaran Fuska Da lalle
 Shin kun san cewa amfani da lalle ko ruwansa na taimakawa wajen gyaran fata da kuma magance cututtukan fata? Lalle na dauke da sinadaran bitamin C da K don haka, yana magance amosanin ka da kara cikar gashi da kuma dada tsawon gashi. Lalle na kara hasken fata da kuma sanya sulbinta. Idan ba a damu da amfani da shi ba, ya kamata a fara domin amfana da shi.

• kurajen fuska: Idan kuraje musamman kanana masu yawan naci suka feso a fuska, a samu garin lalle sannan a zuba tafasasshen ruwa kadan a ciki da man zaitun da kuma gunduwar kwai sannan a kwaba sai a shafa a fuska na tsawon minti goma zuwa sha biyar sannan a wanke. Yana da kyau a rika yin haka kamar sau daya a mako domin samun fata mai sulbi.

• Don kwalliya: A samu jan lalle a kwaba da lemun tsami da man lalle sannan a shafa a tafin kafa ko fata na tsawon awa uku sannan a wanke da ruwa. Yin hakan na kare mutum daga sihiri da kuma gyara fatar tafin hannu da kuma ta kafa.

• Amosanin ka da cikar gashi: A kwaba lalle da dan ruwa amma ba sosai ba sannan a tsaga gashin ka a zuba a fatar kai kowane sako sannan a rufe gashin da leda na tsawon minti talatin sannan a wanke da ruwan dumi da kuma man wanke gashi domin samun cika da tsawo da kuma warkar da amosanin ka.

• Hasken fuska: A samu ruwan lalle sannan a rika shafawa a fuska a kullum da auduga kafin a shiga wanka. Yana da kyau idan an shafa ruwan a fuska sai a rika dada wani ruwan a kan fuskar da zarar ya bushe har tsawon minti goma domin samun sakamako mai kyau sannan a wanke fuska a shiga wanka. Za a iya yin wanka da ruwan lalle idan amarya ce ana shirin yin aure domin dada hasken fatar baki daya.

• Man lalle: Amfani da man lalle a fatar kai ko lokacin kitso ba karamin dada tsayin gashi yake yi ba. Za a iya samun man gashin kai a manyan shagunan da ke sayar da  man kwalliya. Za a iya ganin sakamako cikin mako biyu zuwa uku da fara amfani da hadin

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA