Kannywood

Dalilin da yasa na jawo mata ta harkar fina-finan Hausa – Jarumi Haruna Talle Maifata

Haruna Talle Maifata, jarumi kuma babban darektan kamfanin shirya fina-finai na Maifata Movies, haifaffen garin Jos, jihar Filato ya bayyana matukar sha’awar sa ga sana’ar sa da ta kai shi ga jawo matar sa cikinta.
Yayin wata hira da jaridar Daily Trust, Maifata ya ce ya shiga harkar fim ne saboda sha’awar sa ga fina-finai musamman yadda take daga sunan mutum mayar da shi fitacce a cikin al’umma.
Da yake amsa tambaya a kan ko yana fuskantar kalubale tsakaninsa da matar sa a kan harkokin sana’ar sa, Maifata ya amsa da cewar akwai jituwa, yarda da fahimtar juna tsakaninsa da matar sa.

Bari na fada maka wani abu; gidana babba ne da dakuna da yawa, wani lokacin a nan nake saukar jarumai mata idan a Jos nake shirya fim.

“Mata ta bata taba yin korafi da hakan ba, hasali ma ita ce ke dafa masu abinci. Akwai fahimtar juna tsakanina da mata ta, ta yarda da ni kuma ta san ba zan iya cin amarta ba.
“Bari ma na fada da baki na cewar nine na jawo mata ta cikin harkar fim; na bata kudin da ta dauki nauyin shirya fina-finai har guda biyu kuma na kawo ta Kannywood ne domin nuna mata irin ribar da ake samu a harkar sannan ta san babu wani abu da nake boye mata ,” kamar yadda jarumin ya fada a cikin hirar tasa da Daily Trust.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button