Kannywood

An kama Darakta Shirya Fina Finai Sanusi Oscar 442 Zuwa Gidan Yari

Saga jiya zuwa yau dai shafin Hausaloaded ya samu labarai wanda sunka tabbatar da cewa ankai darakta Sanusi oscar 442 gidan oscar wanda munka samu martani sosai kadan daga cikin jarumai ko muce mawakan wannan masana’atar kannywood.

Ga jawabin Shahararren mawaki Aminu Abubakar Ladan Ala

“A yanzu ka taka babban Mataki wanda ba duka Ido ke iya hangensa ba. Idan akwai matsala a shiga kurkuku bata wuce Dalilin Shigar ka ba. In ya zamo an kaika ne bisa zalunci Karka damu ka saurari sakamakon da Allah zai maka a kan duk wanda ya zalunce ka. Ina yi maka jajen wannan Halin Rayuwa kuma ina yi maka murna da Alkhairi da zai biyo bayan kaskanci.@Sanusi Oska.”

Martani Babban Darakta Falaku Dorayi

“A dubi masalahar zaman lafiya ai masa adalci Dan Allah.
#kanostatecensorshipboard
Kafin SIYASA sunan mu Yan Kannywood. Kar mu bari SIYASA tai tasiri wajan raba kawunanmu.

Nafi ganin Dan film Dan uwa mafi kusa dani akan Dan siyasa.

Allah ya hada kawunanmu.”

Martanin shalelenmawaka

“Babu komai wlh komin nisan dare gari zai waye.
Ina dai bada shawara arika sara ana duba bakin gatari.
Bamuji dadin wannan abuba kuma abin kunya ne  ace mutun da wayan sa ya rika sallah babu alola. @kwankwasiyya_nigeria  #FreeOscar442″

Martanin Jarumi Adam a  Zango shima

“KA SAKE SAMUN SABUWAR ILIMI.@sunusi_oscar__442 .
Kayi hakuri dan uwa babu abinda baya wucewa. Wata rana yadda nake bada labarin shiga gida yari, kaimu haka zaka bada. “

Ku kasance da Hausaloaded.com domin zamuci gaba da bibiyar wannan labari domin kawo muku dalilai da kuma sannin gaskiya wanda ya kaishi gidan yari.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button