Uncategorized

Me Yana Aure Dadi ?

A kasar Hausa, maganganu irin su “Aure yakin mata” dadaddu ne kuma sanannu. Abin da a mafiya yawan lokaci tun kafin matar ta shiga gidan auren yake alamta ma ta cewa, auren nan fa ba abin dadi ba ne. Hasali ma dai yaki ne, don haka ta shiga da shirinta. Haka nan shi kansa namijin yayin da a ka ce yau an daura wa wane aure, sai a ce ‘ya kwanto kura!’ Wasu ma har da kari, wai ba takunkumi. To ta yaya ne kuwa za mu iya danganta mutumin da ya kwanto kura da samun zaman lafiya?

Amma kuma abin mamaki a gefe guda idan za ka kalli babban ko kuma daya daga mafiya girman dalilan da Ubangiji subhanahu wa ta’ala ya shardanta gina aure a kansu, sai ka taras shi ne samar da nutsuwa ga ma’auratan. Bayan ma an sami nutsuwar har da soyayya da jin kai ko tausayawa juna. Haduwar soyayya da jinkai da nutsuwa kuwa shi ne wani yanayi wanda duk duniya babu wani yanayi da ya kai shi dadi! Kuma duk duniyar babu inda za ka same shi sai a garin aure! To amma idan haka ne, “Me Ya Hana Aure Dadi?”
Akwai tambayoyi da ya kamata a ce muna yi wa kanmu, ko da dai wasu ba su tambaye mu ba. Kuma ko da dai mu ma ba mu sami wadanda za mu yi wa su ba. Domin idan har mun ja baki mun yi shiru, to fa tabbas ko dai mu cutu, ko mu cika da rudu da rashin kwanciyar hankali. Daga karshe ma kuma abin ya iya wuce kawunanmu, illarsa ta kai har ga tsatson da muke sa ran za su taso su maye gurabenmu nan gaba. Misali, lemo ka nufi sha, irin tanjirin din nan, wanda tun ma kafin a gama yankawa a miko maka ka fara hadiyar yawu. Amma kuma ana mikowa da ka sa a bakinka sai ka ji tsananin tsami! A irin wannan yanayi, idan har ka kasa daga kai ka kalli wanda ya ba ka lemon nan ka ce masa “Ya aka yi na ji tsami?” Tunda dai kai ka tabbata ba na tsamin ka bukata ba. To ya kamata ka tambayi Kanka, me ya kawo tsamin ciki. Domin abu ne da ba tsammani, kuma kai da kanka ka san ba shi ka tafi nema ba tun asali. To kamar haka ne kuma bai kamata mu ja baki mu yi shiru a cikin maganar yadda aure ya dena dadi yanzu ba. Domin abu ne idan an bar shi a hakan zai iya zarcewa daga kanmu har kan na bayanmu.

Abu mafi muhimmanci kuwa shi ne, bayan mun yi tambayar mu nemo amsa ko amsoshin. Sannan bayan mun nemo amsoshin mu yi aiki. Wato mu yi kokarin sauya abin da zai sauyu, mu debe abin da dama tarkace ne kawai ba shi da wani amfani. Mu kuma shigo da manda muka ki shigo da shi, alhalin mun san shigo da shi din shi zai fi taimakon mu. Sannan mu dawo da wanda a baya yana ciki mu ka dauke shi, tare da cewa mun tabbata yana taimaka mana a cikin tafiyar. Muna rokon Allah Ya katarshe mu zakulo abubuwan da za su amfane mu baki daya. Ga wasu daga cikin amsoshin tambayoyi:

1. Wa Ya Kamata In Ajawai

Zabi shi ne mataki na farko, kuma mafi muhimmanci a cikin sha’anin aure. Wanda daga shi ne ake iya hasashen ina auren ya nufa, ina zai iya kaiwa, kuma daga ina zai iya wargatsewa. Wannan shi ya sa manya ba su cika yarda da kawai mutum ya zo sama ta ka su dauki yarsu su ba shi, ko kuma su su bar nasu dan ya dauko musu wata da ba su san komai game da gidansu ba. Domin idan har aka ce mutum ya yi rashin sa’ar samun abokin zama, to fa wannan mutumin ya shiga wata rayuwa ce ta kunci, wadda idan ba tsananin dace ba, har a bada ba zai taba dawowa hayyacinsa ba.

Dukkan zabi kuwa da mutum zai yi, a matsayinsa na musulmi ko a matsayinta na musulma, to dole ne ya kasance bisa la’akari da koyarwa da shawara da kuma shiryarwa irin ta Annabi sallallahu alaihi wa sallam. Na tabbata da yawan mu muna sane da cewa akwai nuni da aka yi ga maza kai tsaye cikin matar ko irin matan da su ka kamata su aura. Haka nan su ma matan akwai irin wannan nuni da aka yi musu. Don haka ba mu da wata hujja da za mu ce mun afka rami ne bisa tsautsayi. Amma mu kalli me ya kore nutsuwa a cikin zaman aure tukun, kafin mu kara waiwayar wannan fanni.

Me Ya Hana Ma’aurata shisuwa?

Daya daga cikin manyan dalilan kulla auratayya tsakanin maza da mata, kamar yadda mu ka ambata tun farko, shi ne samar da nutsuwa tsakanin mata da mijin. Amma abin da da yawanmu, musamman matanmu ba su sani ba shi ne, nutsuwar mace tana `danfare ne da nutsuwar mijinta. kenan idan har shi namijin bai sami nutsuwa a gidansa ba, to tabbas wannan matar ma ba za ta taba samu ba.
Yayin da Ubangiji Mabuwayi ya nufi ambatar wannnan babbar manufa ta aure, sai Ya ce, a cikin Al Kur`ani mai tsarki:
“Shi ne (Allah) wannan da ya halicce ku daga rai `kwaya `daya (ran annabi Adam a.s). Sai Ya sanya wa wannan ran matarsa daga jikinsa.(Domin daga hakarkarin annabi Adam aka samar da matarsa Hauwa). Domin ya sami nutsuwa zuwa gare ta.
A wata ayar Ya ce:
“Kuma yana daga cikin ayoyinSa, Ya halitta muku matanku daga jinsinku (na mutane), domin ku rika samun nutsuwa zuwa gare su. Sannan kuma ya sanya soyayya da jinkai a tsakaninku…”

ko kamar yadda ya ce Subhanahu wa ta`ala.
Kamar yadda za mu iya gani a wa`dannan ayoyi masu albarka guda biyu. Ana dangana samun nutsuwar ne ga namijin ko mazan. Ba wai saboda nutsuwar macen ba ta da muhimmanci ba, sai don tabbatar da cewa samun nutsuwar matar yana da alaka ne da samun nutsuwar mijinta. Wato yayin da duk namiji ya sami nutsuwa a gidansa, to fa tabbas wannan matar tasa za ta samu nutsuwa, haka kuma yayin da duk ya rasa nutsuwa ita ma duk `kulumbotonta ba ta isa ta samu ba. Sai dai kamar haka ne kuma kan faru ga mijin da ya hana matarsa nutsuwa da gangan shi ma.

Kodayake, mutane da dama sukan yi tsammanin nutsuwa a inda kuma sam ba ta wurin. Na sani watakila wasu su yi tsammanin samun nutsuwa a wurin matar da ta yi wasu `yan dabaru ta mallake miji tana juyawa tare da cutar da shi yadda take so. Ko mijin da ya karkarta ga matarsa `daya ba bar dayar tana cutuwa, da makamantan wadannan. Maganar gaskiya ita ce, wadannan mutanen suna wata rayuwa ce irin ta `dan `baure, daga waje fes, amma zukatansu cike da damuwa. Don haka wadda duk da gaske take son nutsuwa a rayuwarta, ta bi hanyoyin samar wa mijinta nutsuwa.

Za mu dora a makon gobe insha Allahu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button