Politics Musics
Muhammadu Buhari Ya Nada Rarara A Matsayin Daraktan Wakoki Na Kasa
Advertisment
Fadar shugaban kasa, ta ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya ta nada shahararren mawakin nan na Kano, Dauda Rarara a matsayin daraktan waka na kasa kan kwamitin magoya bayan Buhari a 2019.
Babban mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin lamuran siyasa, Gideon Sammani, wanda ya bayyana akan a wata sanarwa yace kwamitin zai samu jagorancin tsohon shugaban PDP na kasa, Ali Modu Sharif a matsayin darakta janar.
Sauran wadanda aka nada a kwamitin sun hada dad an wasan Nollywood kuma dan majalisar jihar Lagas Hon Desmond Elliot a matsayin babban sakataren labaran kwamitin na kasa, da kuma shugaban ma’aikata na gwamnan jihar Imo kuma dan takarar gwamna a APC, Uche Ugwumba Nwosu a matsayin babban sakatare.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com



![[MUSIC] Rarara - Banza 7 Ta kasa Amo](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2021/03/real_dauda_kahutu_rarara-20210302-0001-1.jpg?resize=390%2C220&ssl=1)

