Har Yanzu Ba Mu Gano ‘Yan Madigon Da Ake Yayata Hotunan Su Ta Kafafen Sadarwa Ba, Inji Sheikh Daurawa Shugaban Hisba Ta Jihar Kano
“Tun bayan bayyanar faifan Bidiyo wanda ke dauke da yadda wasu Balagaggun Mata ke gudanar da badala ta hanyar yin madigo kiri kiri, wadanda aka danganta su da jihar Kano, hukumar mu ta hisbah ta zage damtse wajen bincikowa domin kamo wadannan Mata, sai dai har ya zuwa wannan lokaci da muke ciki mun gagara samun su, kuma ina amfani da wannan dama wajen kira ga jama’a cewa, duk wanda ke da masaniya akan inda za’a gano wadannan Mata, to hukumar Hisbah na maraba da shi”.
Wadannan kalamai sun fito ne daga bakin shugaban hukumar Hisba ta jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, a lokacin bikin kaddamar da Jami’an tsaro masu kula da masallachin Juma’a na Sultan Bello dake Kaduna, wanda ya gudana a harabar masallachin a ranar Juma’a.
Sheikh Daurawa ya cigaba da cewar, aikin hukumar su ta Hisba shine tabbatar da bin tsari da dokokin Shari’ar musulunci, saboda haka ba za su saurara ma kowa ba muddin ya karya dokar Islam, kuma raddi ne ga masu zargin hukumar da cewar tana kawar da kai ga wasu, sannan tana hukunta wasu.
A ‘yan kwanakin baya ne wani faifan bidiyo ya bayyana a kafafen sadarwa na zamani na wasu ‘yan Mata dake madigo, kuma wadanda aka tabbatar da cewar ‘ya’yan manya ne daga Kano, sannan a ka zargi hukumar Hisba da yin shakulatin bangaro akai.
Sources:Rariya