Labarai

Kallon fim din batsa ya saka shi yiwa mahaifiyar sa fyade

Wani matashi mai mayatar kallon fina-finan batsa ya shiga hannun hukuma bayan ya yiwa mahaifiyar sa fyade a kasar Indiya.

Matashin, Rohan; mai shekaru 22, ya lallaba dakin mahaifiyar sa da tsakar dare tare da daure mata baki yayin da take kwance tana bacci.

Bayan mahaifiyar sa ta farka sai Rohan ya wayance da cewar yana neman ruwa ne kafin daga bisani ya haike mata.

Makwabtan su sun ce sun ji ihun mahaifiyar matashin a yayin da take kokarin neman taimako, sai dai makwabtan basu kira ‘yan sanda ba saboda yawan samun fada a gidan.

Makwabtan su sun tabbatar da cewar Rohan na yawan kallon fim din batsa a wayar sa.

Kazalika ‘yan sanda sun ce Rohan kan raba dare yana kallon fim din batsa, wasu lokutan ma a gaban mahaifiyar sa da ‘yar uwar sa.

Mahifiyar sa ta sanar da mijin ta da babban dan ta kafin daga bisani su shigar da korafi a ofishin ‘yan sanda. Kazalika, ta sanar da ‘yan sanda cewar ya sha yunkurin haike mata a baya.

Jami’in ‘yan sanda, S M Rabari ya ce: “Mun kama Rohan kuma mun aika shi da mahaifiyar sa asibiti domin gwaji.”

Sources :Naij.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button