INDA RANKA: Yadda Ake Tono Matattu A Kasar Indonisiya Domin Yin Bikin Tunawa Da Su (Hotuna)
A yankin TORAJA dake kasar Indonesia su na da wata al’ada ta hako ‘yan uwansu da abokan arzikin da suka mutu tsawon lokaci don bikin tunawa da su da zaman tare da aka yi da su a lokacin da suke raye.
Sources: Facebook |
Sources: Facebook |
A bikin wanda ake kira MA’NENE, a kan je kaburburan matattu a kwakulo gawawwakinsu tare da goge su, da shafe su da mai, sannan a duba suturar da aka sanyawa mamaci a lokacin da yake raye, ko kuma a nemi wata sabuwa a sanya masa.
Sources: Facebook |
Sources: Facebook |
‘Yan uwa da abokan arziki sukan halarci wannan bikin, a kan yi labaru da tunawa da rayuwar da akayi da mamaci a lokacinda yake raye, sannan aci abinci, wani lokaci a sha sigari idan ya kasance mamacin yana shan sigari a lokacin da yake raye don tunawa da irin rayuwar akayi dashi a lokacinda yake raye.
Sources: Rariya |
Su dai wadannan mutane su na amfani da maganin da ke hana Gawa lalacewa ne a tsawon shekaru.
Allah ka kara bamu hasken musulunci.