Labarai

Allahu Akbar : Miji da mata da yayan su biyu sun mutu sanadiyar gobara

Innalillahi wainna ilaihi rajiun: Da ita da mijinta da ya’yanta 2 sun mutu a gobara a daren jiya

Wannan mata mai suna Bilkisu M Sani da mijinta da ya’yansu su 2 duka sun mutu a gobarar da ta tashi cikin daren jiya a Zaria

Hotunan mijin da yayansu.Allahu Akbar : Miji da mata da yayan su biyu sun mutu sanadiyar gobara
Allahu Akbar : Miji da mata da yayan su biyu sun mutu sanadiyar gobara
Miji da mata da yayansu sun mutu a gobara

Muna rokon Allah ya jikansu yayi musu rahama amen.

Wani labarin: Gobara Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Miji Da Matarsa, Wadanda Dukkansu Likitoci Ne

Waɗannan ma’auratan, sun kasance likitoci, kuma suna aiki ne a asibitin UMTH dake Maiduguri jihar Borno. Sun rasu ne bayan da gobara ta kama gidansu.

Da farko mijin mai suna Dr Auta ne ya fara mutuwa, washegarin safiyar ranar Laraba ita ma matar, Dr Amina ta rasu.

Majiyar ta bayyana cewa an binne marigayi Dr Auta Gidado daidai da koyarwar musulunci bayan an sallaci gawarsa a masallacin UMTH.

Majiyar ta ci gaba da cewa: “Kasa da sao’i 24 bayan mutuwar mijin, mun kuma rasa Dr Amina Ahmad a safiyar yau (jiya). Mun samu sakon da misalin karfe 3:00am.”

Yayin da yake tabbatar da lamarin, Shugaban kungiyar likitocin UMTH, Dr Abdullahi Usman, ya nuna bakin ciki kan mutuwar ma’auratan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button