Addini

VIDEO : Ku Nemi Tsarin Allah Daga Fitina Ta Fili Da Ta Boye ~ Dr Bashir Aliyu Umar

Taken Huduba: Ku Nemi Tsarin Allah Daga Fitina Ta Fili Da Ta Boye ~ Dr Bashir Aliyu Umar
Fitina shi ne abin da yake kawo quna, Malamai sun ce fitina shi ne abin da yake kawo kisan kai da sauran abubuwa na tada zaune tsaye.
Annabi SAW ya sanar da sahabbansa cewa alamar karshen duniya akwai kisan kai, rikice-rikice da fitintinu.
Manzon Allah SAW yace fitintinu za su zo, wanda yake tsaye ya fi wanda yake tafiya a cikinta, wanda yake zaune ya fi wanda yake tsaye.
Fitina a gwame take da shaidan saboda cutuwa da sharrin da yake cikinta.
Malamai sun kwadaitar da cewa lokacin da fitina ta fara afkuwa ake yawaita tunatar da cewa, fitina ko yaqi kafin a fara tamkar budurwa ce kyakkyawa amma da zarar an fara sai kaga ta koma tsuhuwa tukuf ko hakori babu a bakinta.
Shaidanu na mutane da aljanu suna ingiza fitina suna yada ta da dukkan karfinsu domin samun barnar da za ta zo a karshe.
Duk wani abu da mutum yake nema ta hanyar fitina to ba zai samu biyan bukatarsa ba.
Muna da misalai masu yawa akan irin wannan fitina ga su nan birjik. Mu duba kasar Libya, sai da ta kai cewa kusan kowa a Libya yana zaune ne a cikin gidansa ba gidan haya ba. Suna cikin yalwar tattalin arziki da kwanciyar hankali. Amma aka suranta musu cewa sai sun tada fitina, sai sun nemi yanci da sauransu. A karshe ga su nan yanzu ba zaman lafiya ba aminci ba kwanciyar hankali da yalwar arziki.
Fitina tana kawo karyewar tattalin arziki, na ga mutum a Saudiyya dan asalin kasar Syria wanda yake da babban kamfani karkashinsa akwai mutum sama da 200 da suke aiki a kamfaninsa amma saboda fitinar da ta faru a Syria ta sa ya dawo Saudiyya yana yin kabu-kabu da mota.
Ko shakka zuluncin shugabanni akwai shi amma ka’idar Musulunci ba a kawar da barna da barna, Musulunci ya hana mu aikata barna saboda gudun barna mafi girma.
Annabi ya so ya rusa Ka’aba saboda ya mayar da ita kamar yadda Annabi Ibrahim ya yi ta, amma saboda Annabi yana tsoron babbar barna za ta iya faruwa sai ya hakura.
Bin hanyoyi na lumana domin kawar da barna shi yafi sama da bin hanyar tada zaune tsaye.
Masana sun tabbatar da cewa hanya mafi sauki ta kawo fitina ko barna shi ne ta hanyar zanga-zanga.
Addininmu ya yi mana gargadi akan fitina.
Sau da yawa magauta ba sa samun cinma wata manufa ko buri sai ta hanyar tada fitina.
Wannan kasa ta mu Allah ya yi mana ni’imomi masu yawa. Akwai masu neman wannan kasa ta mu da sharri.
Matasa ku ne za ku hayayyafa nan gaba, za kuyi iyali to yaya kuke so yayanku su taso nan gaba bayan kun rusa kasa kun kawo rudani a kasarku?
Kasar Sudan itama misali ce na abin da fitina take kawowa.
Annabi yace ku nemi tsarin Allah daga fitina ta rana da ta dare, fitinar Dujal, fitinar azabar kabari.
Babu wata kasa da fitina ta taba kawo alheri ga kasar.
Musulmi Allah ya ba mu ilimi da haske na Alqur’ani da sunnar Manzon Allah SAW. Mu zamanto masu hankali da hangen nesa
Muna kira ga Gwamnati cewa Lallai abubuwan da suke cewa za su yi musamman na matasa su tabbatar sun yi, maganar da shugaban kasa ya fada na ayyukan da aka kirkiro domin matasa to a tabbata an aiwatar.
Kudin da aka ce za a bawa masu masana’antu da kamfanunuwa na wata uku a tabbatar an aiwatar an basu.
Tsarin yin rigista kyauta da gwamnati ta fito dashi ga masu son bude kamfani a tabbatar an yi, sai dai mutum daya ace ya wakilci jiha wannan ya yi kadan ya kamata a sake dubawa.
Allah ka kyautata al’amarin al’ummar Annabi Muhammad SAW. Amin..
 

 
 







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button