An rage farashin Kudin Aure a Jamhuriyyar Niger Daga jaka 50 yanzu ya koma jaka 20
Sarkin Damagaram, Mai Martaba Alhaji Abubakar Sanda, ya sanar da rage farashin sadakin mata A masarautar sa ta Damagaram a jamhuriyyar Nijar
Sarkin ya sanar da hakan a lokacin da ya halarci wani taro na masu ruwa da tsaki,
wanda ya hada da ‘yan kasuwa da kuma kungiyoyin mata a jihar ta Damagaram,
Sarkin ya ce masarautar ta dauki wannan kudurin ne bayan jama’ar garin sun kai masa kukansu akan a sama musu sauki akan al’amuran da suka shafi aure da bikin suna da kuma wasu manyan bidi’oi a yankin jihar. Wanda a cewar sa hakan ya sanya maza basu iya aure sosai kuma mata suna ta karuwa babu mazaje, Sarkin yace wannan ragin zai rage yawan yan mata marasa aure
A yanzu haka dai, masarautar ta garin Damagaram ta rage kudin sadakin aure daga jaka 50 zuwa jaka 20, sannan kuma masarautar ta hana daukan amarya a cikin jerin gwanon motoci, sannan an rage kayan gara, daga karshe kuma an hana yin ankon biki kwata-kwata a jihar. Duk dai da nufin samar da sauki cikin sha’anin aure,
Join Our WhatsApp Channel
Get verified job vacancies, career tips, scholarships and opportunities delivered straight to your phone, free and as soon as they're posted.



